'Na fi jin dadin rawar da na taka a matsayin Mainasara a shirin Labarina’

'Na fi jin dadin rawar da na taka a matsayin Mainasara a shirin Labarina’

Fitaccen dan wasan Kannywood Sadiq Sani Sadiq ya ce bai taba yin farin-jini ba irin wanda ya samu a shirin ‘Labarina’ mai dogon zango tun da ya soma finafinai. Ya bayyana haka ne a hira da TRT Afrika Hausa a birnin Kano na Nijeriya. “Masoyana da yawa sun ma manta da sunana Sadiq Sani Sadiq. Yawanci duk inda nake haduwa da masoyana za ka ji suna cewa Al’amin wasu kuma suna cewa Mainasara. Ba a taba kira na a wayar tarho a kan fim ba kamar wannan (lokaci) na shirin na Labarina ba,” in ji shi. Ya ce masu kallon shirin su shirya sosai domin kuwa nan gaba akwai karin “nishadi da kayatarwa sannan kuma za a yi kuka sosai.” Sadiq ya ce duka matan da aka hada shi da su a fim din wato Maryam da Jamila suna “taka rawar da ta dace” kuma ya ji dadin aiki da su. Ya ce ya fi jin dadin fitowa a matsayin Mainasara “saboda yanayin mutum ne mai kudi matashi” don haka yanayin “yadda na gabatar da kaina, yanayin maganata da tafiyata yadda suka canza. Gaskiya na fi jin dadin lokacin da ya bayyana a matsayin Mainasara" ba Al'amin ba.