‘Ana yawan tambayata addinin da nake yi’

‘Ana yawan tambayata addinin da nake yi’

Tauraro a shirin Kwana Casa’in mai dogon zango, John Dan Daso, ya ce mutane suna yawan tambayarsa kan ko shi Musulmi ne ko Kirista. Ya bayyana haka ne a hira ta musamman da TRT Afrika Hausa a birnin Kano na Nijeriya. John Dan Daso, wanda sunansa na ainihi shi ne Waziri Alhaji Salihu Hong, ya ce “Musulmi ne ni gaba da baya. Ina Sallah yadda Musulmai suke yi.” Ya kara da cewa rawar da yake takawa a matsayin Kirista a Kwana Casa’in ta nuna cewa ya gwanance wajen yin aikinsa tun da har wasu suke yi masa kallo a matsayin wanda ba Musulmi ba. Ya yi kira ga masu kallonsu da su rika yi wa ‘yan fim uzuri bisa wasu kura-kurai da suke aikatawa, yana mai cewa kowa yana iya yin kuskure.