Ana kiran karawa tsakanin Inter Milan da AC Milan "Derby di Milano" / Hoto: Reuters

A yanzu dai ta tabbata cewa tsohuwar hamayya za ta tashi a duka wasannin bangare biyu na dab da na karshe, a cin kofin Zakarun Turai na UEFA.

Kulob hudu ne masu dadaddiyar kullalliya za su kece raini a wasannin, biyu daga Italiya, sai daya daga Ingila, daya kuma daga Sifaniya.

Tun a Talata kulob din AC Milan na Italiya ya fito zagayen dab da na karshe bayan doke Napoli, inda a jiya kuma wani kulob din daga Milan, wato Inter shi ma ya fito zagayen na kungiyoyi hudu.

A ranar Laraba Inter ta sallami Benfica ta Purtugal, duk da Benfica ta yi nasarar rama duka kwallaye ukun da Inter ta zura mata.

Wasan ya kayatar saboda an tashi 3-3, amma Benfica ta tashi a tutar babu saboda a jimlace, Inter tana da 5 Benfica kuma tana da 3.

A yanzu dai za a kara ne tsakanin kulob biyu masu makwabtaka da juna a birnin Milan na Italiya, inda suke buga wasa a fili daya.

Sitadiyon din San Siro ita ce mafi girma a Italiya saboda tana daukar mutum dubu 80 /Hoto: AA

Hamayyar masu buga wasa a sitadiyom daya

Ana iya cewa Inter Milan da AC Milan tamkar taliya ce da macaroni, don dukansu tushensu kasar Italiya ne. Kulob din biyu sun wuce a ce musu makwabta, saboda a filin wasa daya suke buga duk wasansu na gida.

Tun a shekarar 1926 Milan ta fara yin sheka a mashahurin filin wasanan nan na birnin Milan, wato San Siro, wanda shi ne mafi girma a Italiya saboda yana daukar mutum 80,000.

A shekarar 1947, sai ita ma Inter ta mayar da San Siro wajen buga wasanninta na gida. Hakan ya janyo ba a iya saka wa kulob din biyu wasa lokaci daya, idan ba junansu za su fuskanta ba.

Akwai dadaddiyar hamayya tsakanin kulob din AC Milan da na Inter Milan, har ta kai ana yi wa duk wasan da zai hada kungiyoyin biyu lakabi ta “Derby di Milano”, wato karon battar Milan.

A kididdigar tarihin gasanni daban-daban, an gwabza wasanni 235 tsakanin Milan da Inter. Yayin da Inter ta ci wasa 87, Milan ta ci 79, sannan sun yi kunnen doki sau 69.

Kofin zakarun Turai yana da farin jini matuka a fadin duniya /Hoto: AA

Ko a gasar Serie A, kankankan suke wajen yawan lashe gasar sau 19. A bana ma, a yau maki biyu ne rak ya raba su, inda Milan take sama da maki 53, yayin da Inter ke biye mata da maki 51.

A wasannin zakarun Turai na UEFA, kulob din biyu sun kara har sau hudu, inda Milan ta yi nasara sau biyu, sannan aka yi canjaras sau biyu.

Wa zai ciyo wa Italiya kofin zakarun Turai bayan shekaru 13?

Wasan da zai zama na ‘yan gida daya zai yi zafi saboda kowanne cikinsu yana da burin daga kofin zakarun Turai, kuma yau shekara 13 rabon da wata kungiya daga Italiya ta lashe kofin.

AC milan ce ta fi daga kofin na zakarun Turai a duka kungiyoyin da ke Italiya, saboda ta daga har sau bakwai, wanda yake nufin ita ce ta biyu a yawan daga kofin bayan Real Madrid mai kofuna 14.

Inter kuwa sau uku kacal ta taba daga kofin, kuma rabonsu da shi tun shekarar 2010, lokacin da Jose Mourinho ya ciyo musu bayan shekara 45 ba su ci kofin ba.

Yayin da Inter ke karkashin jagorancin Simone Inzaghi tun shekarar 2021, Stefano Pioli, wanda tsohon kocin Inter ne, shi ke jagorantar Milan tun shekarar 2019.

Masoya Milan dai sun fi cika baki inda suke cewa, ‘me jiya ta yi balle yau’, saboda Milan din ta ninka Inter cin kofin na UEFA.

Za a buga wasan na gaba ranar 16 ga watan Mayu, kuma duk kulob din da ya yi nasara zai fito wasan karshe na cin kofin, wanda zai gudana a 10 ga watan Yuni, a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

TRT Afrika