Wasu jerin hare-hare na kwanton ɓauna da fashe-fashe a Jamhuriyar Nijar sun yi sanadiyar mutuwar sojoji akalla 12 tare da raunata wasu 30, kamar yadda rundunar sojin ta sanar a gidan talabijin na kasar a ranar Laraba.
A harin na farko da aka kai a yammacin yankin Tillaberi a ranar Lahadin da ta gabata, ‘yan ta’addar da suka kai ɗaruruwa sun kashe sojoji biyar tare da jikkata wasu 25 a cewar rundunar.
Hare-haren ramuwa ta ƙasa da na sama sun kashe "yan ta'adda fiye da 100", in ji rundunar, ba tare da bayar da karin bayani kan maharan ba.
A ranar Litinin, a yankin kudu maso yammacin Diffa mai fama da tashin hankali, inda ake yawan kai hare-hare daga kungiyar Boko Haram da kuma reshen kungiyar IS na yammacin Afirka, wasu bama-bamai da aka dasa sun kashe sojoji biyar da ke sintiri, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya rawaito.
Wani harin da aka kai a matsayin ramuwar gayya "ya kashe 'yan ta'adda da dama" da ke da hannu a kisan sojojin, in ji rundunar.
A harin na baya-bayan nan, mayakan sabuwar kungiyar ‘yan adawa da ake kira Patriotic Movement for Freedom and Justice (MPLJ) sun kai wani samame a wani sansanin soji a yankin Agadez da ke arewacin kasar.
Rundunar ta ce sojoji biyu ne suka mutu sannan shida suka jikkata a harin na ranar Talata.
Rundunar ta ƙara da cewa, "nan take aka fara gudanar da bincike domin zaƙulo maharan da suka gudu zuwa kan iyakar kasar Libya."
Kungiyar ta MPLJ ta yi ikirarin cewa ta kashe sojoji 14 da Jandarmomi biyu a harin, sannan ta yi asarar mayaƙanta guda biyu.
Ƙungiyar MPLJ, wadda aka ƙirƙira a watan Agusta, wani reshe ne na kungiyar 'yan tawayen Patriotic Liberation Front (FPL) mai dauke da makamai, wacce ke fafatawa da gwamnatin mulkin soji don sakin hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum.