Tsarin barin kasuwa ta yi halinta a ɓangaren man fetur na Nijeriya ya sa farashin na fetur na tafiya daidai da yadda mai yake a kasuwar duniya duk da matatar Dangote na aiki da ƙarfinta.
Farashin fetur ya ƙaru da fiye da kashi 60 cikin 100 a watan Maris kaɗai, wanda shi ne mafi girman ƙaruwa a cikin manyan ƙasashen Afirka.
Matatar Dangote, mafi girma a Afirka, na aiki da cikakken ƙarfinta na gangar mai 650,000 a rana, tare da ƙaruwa a yawan man da take samarwa kasuwar cikin gida tun daga watan Maris, duk da cewa tana ci gaba da faɗaɗa fitar da mai zuwa sauran ƙasashen Afirka inda a halin yanzu take fitar da kusan gangar mai 214,000 a rana.
Da yake bayani kan hauhawar farashin, Manajan Daraktan matatar Dangote, David Bird ya ce kamfanin na samun kusan jiragen ɗanyen mai guda biyar ne kawai a wata daga cikin gida, wanda ya yi ƙasa sosai da guda 13 zuwa 15 da ake buƙata.
