| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Tinubu ya nemi Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince ya karɓo bashin $20.51b da €1.04bn daga waje
Tinubu ya ce rancen ya zama wajibi domin bai wa gwamnatin tarayya damar sauke nauyin da ke kanta ga ’yan Nijeriya da kuma samar da kuɗaɗen gudanar da ayyuka a muhimman fannoni.
Tinubu ya nemi Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince ya karɓo bashin $20.51b da €1.04bn daga waje
Tinubu ya nemi Majalisar Dattawan Nijeriya ta amince ya karɓo bashin $20.51b da €1.04bn daga waje

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da sabon rancen kuɗin waje na dala biliyan 20.51 da Yuro biliyan 1.45 domin cike gibin kuɗaɗen da ke cikin shirin ƙarin rance na gwamnatin tarayya na shekarun 2026 zuwa 2027.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar buƙatar shugaban ƙasar yayin zaman majalisar ranar Talata.

Tinubu ya ce rancen ya zama wajibi domin bai wa gwamnatin tarayya damar sauke nauyin da ke kanta ga ’yan Nijeriya da kuma samar da kuɗaɗen gudanar da ayyuka a muhimman fannoni.

A cikin wasiƙar, shugaban ƙasar ya ce: “Na miƙa a nan shirin ƙarin rancen kuɗin waje na gwamnatin tarayya na shekarun 2026 zuwa 2027, domin Majalisar Dokoki ta ƙasa ta duba tare da amincewa da shi cikin gaggawa, domin tabbatar da fara aiwatar da ayyukanmu ba tare da ɓata lokaci ba.”

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa an tsara shirye-shiryen da ke cikin wannan tsari ne bisa ƙididdigar fasaha da tattalin arziƙi, tare da la’akari da irin gudummawar da ake sa ran za su bayar wajen bunƙasa zamantakewa da tattalin arziƙin Nijeriya.

Ya ce an tsara shirye-shiryen ne domin samar da ayyukan yi, bunƙasa koyon sana’o’i da kasuwanci, rage talauci da kuma inganta wadatar abinci.

A nasa ɓangaren, Akpabio ya ce an riga an tattauna wasu ɓangarorin shirin rancen a baya yayin nazarin kasafin kuɗi, sannan an kuma amince da wani shirin rancen kuɗin waje a wani lokaci da ya gabata.

Ya miƙa buƙatar ga kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da basussukan cikin gida da na waje, tare da haɗin gwiwar kwamitocin kasafin kuɗi da kuɗaɗe, domin su nazarci buƙatar tare da gabatar da rahotonsu ga majalisar cikin mako guda.

Make the lead sharper and clearerReduce repetition around the loan