| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
’Yansandan Zamfara sun kama matashin da ake zargi da yin kira don 'kai hari Enugu' a wani bidiyo
An ga matashin tare da ɗalibai daga makarantun Islamiyya guda biyu da ke ƙaramar hukumar Maradun a jihar.
’Yansandan Zamfara sun kama matashin da ake zargi da yin kira don 'kai hari Enugu' a wani bidiyo
Kungiyar JIBWIS ce ta mika wa 'yansanda matashin.

Rundunar ’Yansandan Jihar Zamfara ta ce ta fara bincike kan wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wanda ake zargin wani matashi a cikinsa da yin kiraye-kirayen kashe Kiristoci, tare da tabbatar wa al’umma cewa za ta kare kowa ba tare da nuna bambanci na addini ba.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, A.M. Bello, ya fitar a ranar Talata, 27 ga Oktoba, 2026, ya ce bidiyon ya nuna wani matashi sanye da yunifom na ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa’ikamatus Sunnah (JIBWIS), reshen jihar Zamfara, wanda ake zargin an ji yana rera waƙar da ke cewa: “Ku ba mu bindigogi mu je mu kashe Kiristoci.”

An ga matashin tare da ɗalibai daga makarantun Islamiyya guda biyu da ke ƙaramar hukumar Maradun a jihar.

’Yansandan sun ce binciken farko ya nuna cewa an ɗauki bidiyon ne a ranar Jumma’a, 23 ga Oktoba, lokacin da ake zargin matashin yana kan hanyarsa ta zuwa Masallacin Aliyu Ibn Abi Thalib, inda shi da wasu suka kasance suna ba da tsaro yayin sallar Jumma’a da wa’azi.

Makarantun da aka danganta da lamarin su ne Nurul Islam Islamiya da Akidatul Sahiha Islamiya, waɗanda dukkansu suke a ƙaramar hukumar Maradun, mai tazarar kusan kilomita 120 daga Gusau, babban birnin jihar.

Rundunar ’yansandan ta ce bayan bayyanar bidiyon, ta tuntuɓi shugabannin JIBWIS na ƙasa da na jihar. Ƙungiyar ta nesanta kanta daga abin da ake zargin matashin ya aikata da kuma abin da ke cikin bidiyon.

Daga bisani, JIBWIS ta kama wanda ake zargin tare da miƙa shi ga rundunar ’yansandan jihar domin gudanar da bincike.

’Yansandan sun bayyana sunan wanda ake zargin a matsayin Umar Ibrahim Gandi Maradun, ɗan Nijeriya kuma haifaffen ƙaramar hukumar Maradun, wanda aka haifa a ranar 15 ga Satumban 2004.

Bayanai na farko sun nuna cewa ya yi karatun firamare a Makarantar Mualledi Model Primary School da kuma sakandare a Government Day Secondary School, dukkansu da ke Maradun.

Ana zargin ya shiga JIBWIS ne a shekarar 2025, sannan kwanan nan ya samu gurbin karatun digiri a fannin sadarwa ta zamani da aikin jarida a Jami’ar Jihar Zamfara da ke Talata Mafara.

Bincike da matakin shari’a

Rundunar ’yan sandan ta ce tana gudanar da cikakken bincike kan lamarin, kuma bayan kammala shi, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotun da ta dace kan zarge-zargen tunzura mutane zuwa tashin hankali, tada hankalin jama’a da kuma yin barazanar aikata laifi.

Ta ce za a yi hakan bisa tanade-tanaden sashe na 77, 78 da 380(b) na dokar Penal Code da ake amfani da ita a jihar Zamfara, gwargwadon hujjojin da binciken zai tabbatar da su da kuma dokokin da suka dace.

Rundunar ta yi Allah-wadai da duk wani aiki da zai iya haddasa ƙiyayyar addini, barazana ga tsaron al’umma ko kawo cikas ga zaman lafiya da zaman tare.

Ta kuma yi kira ga shugabannin addinai, iyaye, masu kula da yara, hukumomin makarantu da sauran masu ruwa da tsaki da su ƙarfafa koyar da haƙuri, mutunta juna da ɗabi’a nagari, musamman a tsakanin matasa.

Haka kuma, ta shawarci jama’a da su kwantar da hankalinsu, su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, sannan su nisanci duk wani abu da zai iya ƙara rura wutar rikicin addini ko kawo cikas ga zaman lafiya.

Kwamishinan ’yansandan ya sake jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, da kuma mutunta haƙƙoƙin kowane ɗan ƙasa ba tare da nuna bambanci ba, ciki har da ’yancin tunani, lamiri da yin addini da kundin tsarin mulki ya tanada.