| Hausa
NIJERIYA
4 minti karatu
Wike ya ce kiwon shanu a cikin birnin Abuja batu ne na tsaron ƙasa
Wike, wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa kai-tsaye da kafafen yaɗa labarai a ranar Litinin, ya ce wannan ƙalubale na buƙatar tattaunawa ta gaskiya da kuma samar da mafita mai ɗorewa.
Wike ya ce kiwon shanu a cikin birnin Abuja batu ne na tsaron ƙasa
Wike ya ce kiwon shanu a cikin birnin Abuja batu ne na tsaron ƙasa / Others

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ya bayyana damuwar da ake nunawa game da ganin shanu suna kiwo barkatai a gefen tituna da sabbin wuraren da aka bunƙasa a Abuja a matsayin “batun tsaron ƙasa.”

Wike, wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa kai-tsaye da kafafen yaɗa labarai a ranar Litinin, ya ce wannan ƙalubale na buƙatar tattaunawa ta gaskiya da kuma samar da mafita mai ɗorewa.

Ya ce: “Ka yi magana kan shanu. Wannan batun tsaron ƙasa ne. Dole ne mu fuskanci gaskiya.”

Ya ƙara da cewa: “Idan ka ga ana ƙoƙarin ɗaukar mataki kan wasu batutuwa, sai wasu su fito suna danganta lamarin da addini ko ƙabila. Amma a faɗi gaskiya.”

Ministan ya bayyana cewa ɗaya daga cikin matakan da gwamnati ta fara ɗauka shi ne ƙarfafa tsarin kiwon shanu a ruga domin cire dabbobin daga cikin birnin.

Ya ce: “Shugaban Ƙasa ya ce, ‘Mu aiwatar da tsarin ranchinkeɓe wuraren kiwo mu ga yadda za mu fitar da waɗannan shanu daga cikin birni.’ Ganinsu a cikin birni abin kunya ne. Ba daidai ba ne, kuma abu ne mara kyau ba.”

Ya ci gaba da cewa: “A ƙasashen da suka ci gaba ma akwai shanu, amma da ƙyar za ka gan su a cikin birane. Ka je Saudiyya, ba za ka ga shanu suna yawo a cikin gari ba.”

Wike ya yaba wa Ministan Bunƙasa Harkokin Kiwo saboda tattaunawar da yake yi da ƙungiyar Miyetti Allah da sauran masu ruwa da tsaki domin magance matsalar kiwon shanu a buɗe.

Sai dai ya amince cewa har yanzu matsalar tana nan.

Ya ce: “Ina ba da haƙuri kan hakan kuma ina ɗaukar alhakin lamarin; har yanzu akwai shanu. Amma ku ma dole ku fuskanci gaskiya.”

Ya ƙara da cewa: “Ba abu ne mai sauƙi kamar yadda ake faɗa ba. Kun san irin matsalolin da ƙasar nan ke fuskanta. Dole ne mu fito mu ce ga matsalar nan, dole ne mu magance ta, kuma dole ne ku ba mu goyon baya.”

Da yake amsa tambaya game da tarin shara a wasu sassan Abuja kamar Jabi da Garki, ministan ya amince cewa irin hakan na iya faruwa a lokacin da ake hutun aiki, amma ya musanta zargin cewa shara ta mamaye birnin.

‘Yan Kasuwar Gefen Hanya

A wani ɓangaren kuma, ministan ya kare matakan da gwamnatin FCT ke ɗauka na korar masu kasuwanci daga manyan mahadar tituna a Abuja.

Ya jaddada cewa an samar da kasuwanni ga ‘yan kasuwa, kuma yin kasuwanci a gefen tituna na haifar da cunkoso da rashin tsari wanda bai dace da babban birnin ƙasar ba.

Wike ya ce gwamnatin FCT na ci gaba da fuskantar suka duk lokacin da ta yi ƙoƙarin aiwatar da dokoki kan kasuwancin da ba bisa ƙa’ida ba, duk da cewa ta samar da madadin wuraren kasuwanci.

Ya ce: “Idan gwamnati ta ce ba a ware wannan wuri domin kasuwanci ba, kuma ta kori masu kasuwancin daga wurin, sai ka ga ana shirye-shirye a kafafen yaɗa labarai ana cewa gwamnati ba ta samar musu da wani madadin wuri ba, alhali ba gaskiya ba ne. Akwai kasuwanni. Ku je kasuwa ku sayar da kayanku.”

Ministan ya jaddada cewa ba za a iya barin ‘yan kasuwa su mamaye mahadar tituna da sauran wuraren da ba a ware domin kasuwanci ba a tsakiyar birni, domin hakan na haifar da cikas da rashin tsari ga mazauna birnin.

Ya ce: “Ba za ku iya zama a nan ba. Babu kasuwa a nan. Me ya sa za ku zo ku tsaya a mahadar hanya kuna sayar da kayanku? Wannan ma wani abin ta da hankali ne ga jama’a.”

A cewarsa, ana buƙatar goyon bayan jama’a wajen wayar da kan mazauna birnin kan muhimmancin bin dokokin da aka kafa domin kiyaye kyawun da martabar Abuja.

Ya ƙara da cewa: “Wannan shi ne babban birni guda ɗaya da muke da shi a Nijeriya. Ba za mu bari a lalata shi ba kawai saboda wani yana cewa yana neman abin da zai ci. Hakan ba zai zama dalili na mutum ya karya dokokin ƙasa ba.”