Kudin-cizo ya tilasta wa Faransa rufe makarantu bakwai sakamakon fargabar bazuwarsa a yankuna daban-daban. Hoto/Getty Images

A ‘yan kwanakin nan, kudin-cizo ya zama wani abu da ake tattaunawa a shafukan sada zumunta tun bayan da ya addabi kasar Faransa.

Kwaron ya bazu a wurare daban-daban tare da tilasta rufe har wasu makarantu a kasar.

TRT Afrika ta yi nazari dangane da wannan kwaron inda ta tattaro bayanai daga hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta Amurka wato CDC.

Mene ne kudin-cizo?

Kudin-cizo wani kwaro ne mai siffar kwai, wanda hanyar samun abincinsa ita ce shan jini zalla na bil adama ko dabbobi a lokacin da suke bacci.

Kudin-cizo launinsa ja ne da ruwan kasa, ba shi da fiffike, kuma yana da tsawon mita daya zuwa bakwai. Wannan kwaron zai iya rayuwa tsawon watanni bakwai ba tare da ya sha jini.

A ina aka fi samun kudin-cizo?

Ana samun kudin-cizo a fadin duniya, tun daga Arewaci zuwa Kudancin Amurka, zuwa Afirka da Asia da Turai.

Duk da cewa a al’adance an fi samun kudin-cizo a kasashe masu tasowa, sai dai a ‘yan shekarun nan kwaron na ta bazuwa a wasu sassa na Amurka da Canada da Birtaniya da wasu sassa na Turai.

An sha ganin kudin-cizo a manyan otel-otel na duniya, kuma tsan-tsan tsaftar wuri ba zai hana shi zuwa ko zama a irin wuraren ba.

Labari mai alaka: Kudin-cizo ya tilasta wa Faransa rufe makarantu

Kudin-cizo na boyewa da rana a wurare kamar cikin katifa da akwatuna da katakon gado, da katakon madubin daki ko wasu wurare da ke kusa da gado.

Bincike ya nuna cewa kudin-cizo yana tafiya tsawon mita 30 da dare amma yana zaune kusan mita uku daga wuraren da mutane ke kwance suna barci.

Shin kudin cizo na yada cututtuka?

Hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta Amurka wato CDC ta ce ba a san kudin-cizo da yada cututtuka ba, sai dai zamansu a gidaje kan kasance abin damuwa sakamakon yadda suke hana jama’a barci.

Hukumar ta ce sakamakon irin yawan susa da ake yi wa fatar jiki idan kwarin sun yi cizo hakan zai iya bude wata kafa ta kamuwa da wata cuta ta daban da jikin dan adam.

Wace irin barazana kudin cizo yake da ita ga lafiya?

Cizon da wadannan kwarin suke yi na yin tasiri daban ga kowa. Idan suka yi cizon, a jikin wani ba a ganin alama, wani kuma alamar kan nuna ta yadda jiki kan yi ja ko ya yi bororo.

Likitoci ba su dauki kudin-cizo wani babban abu mai illa ga rayuwa ba, sai dai idan jikin mutum ya yi bororo sosai sakamakon yawan cizon zai iya sa a je wurin likita.

Yadda ake samun kudin cizo a gida

Kwarin kudin-cizo dai sun kware wurin iya boyewa. Sakamakon yadda suke da siririn jiki, suna iya kutsawa kusan ko ina tsawon lokaci ba tare da sun sha jini ba.

Akasari an fi yin tsarabarsu jikin gida, inda ake daukarsu daga nan zuwa can.

Sukan makale a cikin akwatuna ko kayayyaki ko a jikin tufafi ko katako har su isa inda za su yada zango.

Kwaron yakan bayyana a gida bayan ya hayayyafa tare da addabar mutane da cizo.

Ta ya ake magance shi?

Masana dai sun yi itifakin cewa kudin-cizo yana da wahalar magani, sakamakon ko da an fesa masa magunguna ba su cika kashe shi ba.

Sai dai wasu kan yi amfani da hanyoyi da dama domin rabuwa da shi da suka hada da fitar da kayayyakin da kwaron ya shiga cikin rana, idan katifa ce akan kwara mata ruwan zafi.

Idan katako ne akan fesa masa magani, idan kuma kwarin sun yi yawa a wani lokaci akan jefar da katako da wasu sauran kayayyakin gida bola duk domin rabuwa da shi.

TRT Afrika da abokan hulda