Yadda cin kofato ke da farin jini a Nijeriya
Wata dattijuwa da ta kwashe fiye da shekaru 45 tana sayar da kofato a birnin Katsina da ke Nijeriya, ta ce wannan sana'a ta rufa mata asiri matuka gaya.
Malama Indo Aisha, matar Sani, ta shaida wa TRT Afrika Hausa cewa kofato yana da matukar farin jini tsakanin mutane kuma ana sayensa daga ciki da wajen jihar.