‘Na gaji wanzanci ne saboda babu namiji a cikin ‘ya’yan mahaifina’

‘Na gaji wanzanci ne saboda babu namiji a cikin ‘ya’yan mahaifina’

Wata matashiyar wanzamiya a birnin Kano da ke Nijeriya ta ce ta gaji sana’ar mahaifinta ne domin yi masa biyayya ganin cewa babu namiji a cikin ‘ya’yansa. A hira da ta yi da TRT Afrika Hausa, Hassana Gambo, wadda ita ce shugabar mata wanzamai ta karamar hukumar Nasarawa, ta ce tana aski da shayi da cire beli da bayar da magunguna. Ta kara da cewa mutane da dama suna yi mata gani-gani idan tana gudanar da sana’arta, sai dai ta ce ko aure za ta yi za ta zabi wanda zai amince ta ci gaba da sana’arta ta gado.