Bayanai kan kasuwar Dawanau
Kasuwar hatsi ta Dawanau da ke Kano a arewacin Nijeriya na daya daga cikin mafi shahara a Afirka. An gina ta a 1985 kuma ta zama cibiyar sayen hatsi zuwa bangarorin kasar da ma kasashen waje. Majalisar hatsi ta duniya ta kiyasta cewa Nijeriya za ta samar da hatsi fiye da tan miliyan 21 tsakanin 2020-2023.