A tarihi ba a taɓa samun wata babbar ƙungiya irin Real Madrid ta bar wata babbar gasa ba. / Hoto: AFP

Sakamakon yawan rashin jituwa da ake samu tsakanin Real Madrid da hukumar La Liga ta Sifaniya, rahotanni na cewa ƙungiyar na duba yiwuwar barin gasar kacokan.

Real Madrid na tunanin komawa wata babbar gasa a ƙasar Turai, kamar Serie A ta Italiya, ko Bundesliga ta Jamus, ko Ligue 1 ta Faransa.

Wannan batu na zuwa ne bayan da ake taƙaddama kan dacewar jan katin da aka bai wa ɗan wasan gaba na ƙunguyar, Jude Bellingham a wasan da Madrid ta buga da Osasuna ranar 15 ga Fabrairu.

Cecekuce ya ɓarke a wasan da Madrid ta tashi 1-1 da Osasuna, inda alƙalin wasa, Jose Luis Munuera Montero ya bai wa Bellingham jan katin kai-tsaye, bayan ya zargi ɗan wasan da yi masa kalaman zagi.

Alƙalin ya zargi ɗan wasan mai shekaru 21 da yin amfanin da kalaman zagi gare shi a minti na 39, wanda ya janyo ya kore shi nan take.

Sai dai ɗan wasan ya dage cewa ba a fahimci kalaman da ya yi ba saboda fushi, ba wai ga alƙalin ba.

Abu mai wuya

Yayin da ƙungiyar ke nuna matuƙar damuwa kan alƙalanci wasanni a La Liga, shafin Goal ya ambato wata jaridar Sifaniya mai suna Sport na cewa Real Madrid na duba yiwuwar ƙauracewa gasar La Liga.

Sai dai wannan mataki na cewa Madrid za ta bar La Liga, ba zai zo da sauƙi ba, saboda sai hukumomin FIFA, UEFA, da hukumar ƙwallon ƙasar da suke son komawa duka sun amince da sauya sheƙar.

Jan katin da aka bai wa Bellingham ɗaya ne cikin jerin batutuwa da suka ƙona wa Real Madrid a kakar bana.

A farkon watan nan, ƙungiyar ta shigar da ƙorafi ga hukumar ƙwallo ta Sifaniya RFEF, inda ta ce ana samun “mummunar matsalar alƙalanci" bayan da Espanyol ta doke su da ci 1-0.

A halin yanzu, saboda jan katin da aka ba shi da zage-zagen da ya yi, Bellingham na fuskantar dakatarwa da za ta kai ta wasanni tsakanin 4 zuwa 12, wanda zai iya hana shi wasa har zuwa ƙarshen watan nan na Fabrairu.

TRT Afrika