A Lahadin nan, rundunar 'yan sanda ta jihar Ogun ta tabbatar da rasuwar wani mai shekara 35, ma'aikacin gidan ajiye namun daji da ke ɗakin karatu na tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo Presidential Library, da ke birnin Abeokuta.
Ma'aikacin mai suna Babaji Daule, haifaffen jihar Bauchi ya rasu ranar Asabar bayan zaki ya kai masa farmaki. Babaji shi ne ke kula da zakin a gidan ajiye namun dajin.
Kakakin rundunar 'yan sandan, Omolola Odutola, ya sanar da wannan a wata sanarwa da ya aike wa 'yan jarida yau Lahadi.
Mai kula da zakin ya manta ya saka sakata a a shingen tsare kejin da zakin yake, kafin ya tunkare shi don ba shi abinci.
Rahotanni sun ce wannan ne ya bai wa zakin damar fitowa ya far wa mai kula da shi, inda ya raunata shi a wuya har ya janyo ya rasa ransa.
An ɗauke gawar mamacin an kai ta gidan ajiye gawawwaki da ke asibitin Ijaye General Hospital, inda shi kuma zakin aka harbe shi kafin ya saki mutumin.