Karin kasashe na tsibiri da kuma birane dage bakin teku na fuskantar barazanar nutsewa/TRTAfrika

A watan Nuwamban bara, kasar Tuvalu ta fitar da wani shiri na gina wani kwafi na kasar a intanet ta yadda karamar kasar ta yankin Pacific za ta cigaba da kasancewa cikin manjahar metaverse, idan karuwar yawan ruwan teku ya hadiye ta.

Sanarwar da ta yi a lokacin taron sauyin yanayi na COP 27 da akayi a Masar, ta fito ne daga cikin wani fim na kimiyya da ke bayyana abubuwan daza su iya samuwa nan gaba, da aka fitar daga masana'antar Hollywood.

Amma babu wani abu mai nasaba da almara cikin barazanar dakasashe na tsibiri ke fuskanta kan karuwar ruwan teku – sakamakon dumamaryanayi da kuma narkewar dusar kankarar yankin Arctic.

Dubban kilomita daga Tuvalu, Maxime Georges ya girma yana ganin teku na matsowa kusa da gidansa da kuma murhunsa dumama gidansa a Mahe, daya daga cikin tsibirai 115 da ke kasar Seychelles a tekun Indiya.

“Tasowata a nan, bakin tekun ne wuraren wasanmu,” kamar yaddaGeorges mai shekara 35 ya shaida wa TRT Afrika.

“Kusan shekara 20 da suka wuce, ruwan na da nisa daga filin, amma a yanzu, kamar yadda za ka iya gani yana kara matsowa kan hanyoyinmu.”

Georges na da shago kusa da bakin teku a Victoria – babban birnin kasar Seychelles – inda yake sayar da kayayyaki da jakankuna, ga dubban masu yawon bude ido da ke zuwa tsibirin.

Yayin da karin kasashe na tsibiri da kuma birane daga bakin teku ke fuskantar fargabar nutsewa cikin teku, gwamnatoci da kuma kwararru sun yi gargadi kan masifar da ka iya faruwa.

Kwamitin gwamnatoci kan sauyin yanayi ya yi hasashen cewar matsakaicin karuwar ruwan teku daga shekarar 2100 zai kasance tsakanin inci 8 zuwa 34 ko kuma akalla kusa da inci uku.

Duniyar ruwa!

Ga masunci mai shekara 50, James Jewell, da alama bakin tekunBeau Vallon da ke tsibirin Mahe ya ragu sosai cikin shekarun da suka gabata.

Murjanin karkashin ruwa ya samu matsala saboda sauyin yanayi/AA

Wasu matsaloli suna biye da karuwar ruwan teku – raguwar kifayesaboda rasa murjanin da ake tallafa wa tsiro rayuwar cikin ruwa.

“An haife mu kusa da teku, mun yi rayuwa kusa da teku, mun san komai game da teku,” in ji shi a lokacin da yake magana da TRT Afrika.

“A da can a, akwai kifaye da yawa, amma a yanzu adadinsu na raguwa.”

A shekarun da suka wuce, wasu nau’o’in bishiyoyin da ke kusa da bakin teku sun bace, ya ce.

A karkashin ruwa mai haske da ake iya gani daga sama, murjani – wurin rayuwar halittun cikin ruwa dangin su kaguwa – ya samu matsala saboda sauyin yanayi.

Kungiyar Reef Resilience Network mai fafatukar kare murjani mai duwatsu a teku, ta ce dumamar teku ta El Niño da aka yi a shekarar 1998 ta taka rawa wajen daye murjanin duwatsu na cikin teku.

Wata dumamar teku ta El Nino da aka sake yi a shekarar 2016 ta janyo bala’i.

Dayewar na faruwa ne a lokacin da murjani suka ture gantsa-kuka saboda yanayi na zafi ko kuma datti. Idan suka rasa sinadaransu, za su ji yunwa.

Murjani kuma ya kasance wani shinge tsakanin teku da kasa.

Ga mazauna kasar da suka kai kimanin mutum 98,000 – kashi 90 cikin 100 cikinsu suna zama ne a Victoria – yiwuwar tsibiransu da ke kasa-kasa su shige cikin teku barazana ce ta gaske duk da kokarin gwamnati.

“Gwamnati ta saka wannan ganuwar ruwan da aka yi da kankare domin kare kasa daga teku, amma lokacin da ruwa ya zo, wannan ganuwar ba za ta iya taimako ba,” in ji Mazime Georges.

An gina ganuwar ne a inda ake tunani kan iyaka ne tsakanin bakin teku da kuma kasa. Amma ana muhawara kan ko ganuwar za ta iya jure bugowar iska da ruwa, musamman a wuraren da ke kasa-kasa a bakin teku.

Tsibirin Mahe, alal misali, na da tudun mita 2.5 daga matakin ruwan teku. A nan ne za a yi muhimman kayayyakin more rayuwa na kasar kamar su filin jirgin sama da tashar jiragen ruwa da wurin adana man fetur da kuma hukumomin ba da agajin gaggawa.

Neman mafita

Ana jin tasirin wadannan abubuwan da sauyin yanayi ya haifar akananan kasashe na tsibiri da ke gabashin Afirka.

A kasar Mauritius, teku na matsowa zuwa kasa kuma yana haddasazaizayar kasa a bakin teku yayin da yawan ruwa mai iska ya karu a kasar.

A Sao Tome and Principe, wata iska ta ruwan sama ta tasamma tsibirin a watan Disamban shekarar 2021, lamarin da ya janyo ambaliyar da ba a taba gani ba cikin shekaru 30.

Gwamnati da hukumar muhalli ta Majlisar Dinkin Duniya suna tsara wani shiri na kasar don karfafa tanadinta ga sauyin yanayi.

Dr Nirmal Shah, shugaban kungiyar kare muhalli ta Nature Seychelles, ya shaida wa TRT Afrika cewar karin yawan ruwan sama mai iska, ciki har da guguwa ackasar, na da tasiri kai tsaye a kan karuwar matakin ruwa.

Nature Seychelles kungiya ce wadda ta dukufa kan kare muhalli.

“Za mu iya dauke wasu daga cikin muhimman abubuwan more rayuwadaga teku inda yawancin su suke, amma wannan na bukatar kudi mai yawa,” in jiDr Shah.

Duk da cewar hadaka ta kasashe na tsibiri ta yaba wa assasa asusun tallafa wa kasashen da sauyin yanayi ya yi wa ta’adi kuma su ka kira shi “wani mataki zuwa adalci kan yanayi”, in ji Dr Shah wanda har yanzu yake shakka.

“A gaskiya, abu ne wanda za mu kira ‘fankon bokiti’. Ba mu san yadda zai kasance ba… kudi nawa za a saka cikinsa,” in ji shi.

Ya ce yana da muhimmanci mutane su gane cewar duk da asusun da aka assasa, wasu abubuwa sun bata har abadan.

“Wannan wani abu ne da nake ganin mutane ba su gane da kyau ba. Ana cewa za mu iya kokarin gyara wasu abubuwa kamar su murjani, amma ba za mu iya gyara su ba, an riga an bata su har abada,” in ji ta.

Da alama masunci James ya yarda da hakan, “A a, babu wata mafita, babu wani bakintekun da ya saura. Mafitar kawai ta ce a bar shi yadda yake,” ya ce.

Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince