Maasai

Wannan abu ya zama mai zaburarwa da karfafa gwiwar samar da kayayyakin Afirka da ake bukatarsu a kasar.

Maasai

Nkerandu Ene Tarimia na daya daga cikin masu sayar da kayayyaki ko yaushe a ‘Kasuwar Maasai’. Ta kware wajen samar da kayan ado da ake samarwa da duwatsu.

“Mama Nancy” kamar yadda aka fi kiran ta a kasuwar, ta ce tana hada wadannan sarkoki wa awarwaro da kanta, ta koyi sana’ar daga mahaifiyarta, kuma tana koyawa ‘yarta.

Maasai

Wannan sana’a ta samar da sarkoki da awarwaro da duwatsu na da alaka da kabilar Maasai, Kabilar gidan yarukan Nilo da ta bazu a arewaci, tsakiya da kudancin Kenya da kuma arewacin Tanzaniya. A Kenya, kusan dukkan rukunin mata na nuna kaunar amfani da kayan ado da Maasai suka samar.

Maasai

Farashin kayan nan na farawa daga dala biyu wato kananan kayayyaki zuwa dala 60 na manyan abubuwan. Da yawan matan da suka dade suna wannan sana’a sun dogara da ita ne wajen kula da iyalansu. Suna samun kudi siosai a lokacin da mutane suka sayi kayan da yawa.

Maasai

Masu sayayya na bayyana sun fi son su je kasuwar Maasai su sayi kayayyakin saboda suna samun nau’ika daban-daban da babu irin su kuma a farashi mai rahusa. Wasu na cewa sun fi son sayayya daga nan idan za su je kasashen waje. Suna isar da kayan Kenya ga duniya.

Maasai

Wasu masu sana’ar na samar da kayan ado daga farin karfe da kahon shanu

Maasai

Wasu daga cikin kayan sawar da ake samarwa a wannan waje na tallata “Afirka”. Wasu na sayen su da yawa suna fitar da su zuwa kasashen waje.

Masai

Kasuwar ta zama wajen bayar da kayayyakin Afirka tsanta ga ‘yan Afirka da ma ‘yan kasashen waje.

Maasai

Masu sana’o’in hannu a ko yaushe na ta kokarin samar da sabbin nau’uka don samun nasarar gasar da suke yi.

TRT Afrika