Daga Coletta Wonjohi
A shekarar 2021, Khaleed Abubakar ya saka na’urar makamashin solar a gonarsa da ke Kisarawe, a kauyen da ke kilomita 100 daga Daresalam, cibiyar kasuwancin kasar Tanzaniya.
Yana bukatar solar ne don kunna fitilun tsaro da kuma jan ruwa daga burtsatsai don ban-ruwa a gonarsa.
Ya fada wa TRT Afrika cewa, “Na kashe kusan dalar Amurka 2,000 wajen sayen allunan solar, da kwambata, da kuma injin ban ruwa. Kayayyakin akwai tsada.
Sai dai kuma ya shiga takaici matuka yayin da injin janyo ruwan nasa ya lalace, kwanaki uku kacal bayan ya saka shi.
Khaleed ya kara da cewa, “Matsalarmu ita ce an cika kasuwanninmu da kayayyakin hada solar marasa inganci, wadanda aka shigo da su daga waje.
"Lokacin da injin ruwan nawa ya lalace, dole na sayo wani, wanda shi ma bai jima ba ya lalace.”
A kasar Kenya da ke makwabtaka, Patrick Babu shi ma bai dade da saka solar a gidansa da ya gama ginawa ba.
Patrick ya fada wa TRT Afrika cewa, “Gaskiya ne cewa hada solar yana da tsada sosai. Na kashe har dala 5,000 kafin na hada solar da ta wadaci gidana gabaki daya, har da injin ruwa.”
Amma fa sai da Patrick ya nemi bashin kungiyar adashe kafin ya iya hada solar.
Ya kara da cewa, “Lokacin da nake sayo kayayyakin hada solar, na fahimci cewa daga waje aka shigo da kayayyakin, wanda watakila ya janyo suka yi tsada.
Wata matsalar ita ce jahiltar yadda ake gane kayan solar masu inganci.
“A karshe na sayo allunan solar da tunanin dukansu iri daya ne. Ina ganin babbar matsalarmu ita ce ba mu da kamfanonin kera kayayyakin solar.”
Hukumar Makamashi ta Duniya ta ce duk da cewa kashi 60% na albarkatun makamashin hasken rana yana Afirka, nahiyar a yanzu tana da karfin samar da kashi 1 cikin 100 ne na makamashin solar.
Ilimi daga kwararru
Turkiyya tana da yalwar albarkatun hasken rana sakamakon yanayin yankin da kasar take.
Shirin Hukumar Makamashi ta Turkiyya na 2022 ya yi hasashen cewa zuwa shekarar 2035, kasar za ta kai matakin samar da makamashin hasken solar gigawatt 52.9.
Kungiyar kwallon kafa ta Turkiyya, wato Galatasaray ta samu kyautar kambun Guinness World Records, saboda saka allunan solar a rufin filin wasanta.
Rufin sitadiyam din yana dauke da sama da allunan solar 10,000 da suke iya samar da wutar lantarki megawatt 4.2.
Turkiyya ta gina tashar makamashin solar mai samar da megawatt 5 a wani fili mai fadin murabba’in mita 100,000 a Dagbeli, wani yanki da ya yi suna wajen samar da ‘ya’yan itace.
Yankin na Dagbeli yana lardin Antalya, gari mafi farin jinin yawon bude ido a Turkiyya, wanda kuma yake gabar tekun Bahar Rum.
Tashar solar za ta samar wa manoma 60,000 makamashi kyauta, wanda za su yi amfani da shi wajen noman rani.
Turkiyya ta baje kolin fasahar makamashin solar a yayin Baje Kolin Fasahar Makamashin Solar da aka yi a Istanbul cikin watan Afrilu.
Taron baje kolin ya janyo ‘yan kasuwa daga China da Indiya da Jamus.
Tolga Borekci, manajan fasaha a Avenof, ya fada wa TRT Afrika cewa, “Za a iya rage farashin solar idan muka samar da abubuwan da ake bukata a kasa.
"A Turkiyya muna amfani da sabbin fasahohi da suke saukaka wa masu amfani da solar.”
Avenof wani kamfanin Turkiyya ne mai zaman kansa, wanda yake kera batiran adana wutar solar.
Robbie Wang shi ne babban manajan Dongjin Longevity Ltd da ke Bangladesh, wanda yake kera batiran solar a kasashe takwas a duniya.
Ya ce, “Kamfanoni da yawa a duniya suna samar da batira kamar mu.
Wang ya fada wa TRT Afrika cewa, “Sakamakon haka masu amfani da solar suna da zabi daban-daban da farashi mabambanta.
A yau mutum zai iya sayen solar cikin saukin da bai fi rabin rabin farashin da ya siya a ‘yan shekarun baya ba.”
Hasken rana yana Afirka
A cewar Majalisar Tattalin Arziki ta Duniya, nahiyar Afirka ta wuce ka’idojin da ake nema wajen samar da solar.
Alkaluman sun nuna cewa nahiyar tana da ikon samar da makamashin solar mai dorewa, wanda zai iya wuce kilowatt 4.5 duk rana.
Kasashe kadan ne a Afirka suka zuba jari a harkar samar da solar. Sun hada da Masar, da Afirka ta Kudu, wadanda suke kan gaba. Sauran kasashen su ne Maroko, da Nijeriya, da Kenya, da Habasha.
Patrick Babu ya bayyanawa TRT Afrika cewa, “Idan gwamnatocinmu za su iya taimakawa wajen tallafar kamfanoni masu zaman kansu, su iya samar da kayayyakin hada solar cikin kasashenmu. Wannan zai taimaka matuka wajen sanya mutane su rungumi solar.”
A wani shirin Bankin Raya Afirka mai suna “Desert to Power”, an tsara tallafawa kasashe 11 na yankin Sahel, da Gabashin Afirka su samu solar.
Shirin bankin na baya-bayan nan a Eritrea yana taimaka wa kasar ta samar da megawatt 30 na solar.
Asusun Lamuni na Duniya ya ce kasashen Afirka ‘dole su saka kaimi don janyo kamfanoni masu zaman kansu su saka jari a harkar makamashi na zamani’.