Daga Mamadou Dian Barry
Yayin da wayoyin hannu na zamani suka zama ruwan dare, kuma intanet mai sauri take samuwa a lungu da sako, fasahar zanen sirri ta QR code (Quick Response) ta samu yaduwa a Afirka.
Babban dalilin yaduwa fasahar QR ita ce amfani da ita a hada-hadar tafi-da-gidanka da kasuwancin intanet. Amfani da fasahar ya watsu matuka a nahiyar.
A Senegal, wani rukunin matasa ya mika shawararsa ta kokarin mayar da wasu harkokin gudanar da gwamnati, su koma masu saukin samu ta hanyar amfani da wannan fasaha.
Kamfanin Japan mai suna Denso Wave ne ya kirkiri fasahar lambar sirri ta QR. Fasahar tana amfani da zubin hoton zanen sirri mai kusurwa biyu, wanda aka zayyana shi ta amfani da kwayoyin pixel masu kusurwa hudu.
Fasahar na ba da damar fassara sako ta hanyar yin sikanin dinsa cikin ‘yan dakikoki. A yau, ana amfani da fasahar a fannoni daban-daban.
Yadda wannan fasaha take kawo gagarumin sauyi ne ya sa wani sabon kamfani a Senegal mai suna Art’Beau-Resecence, yake yunkurin amfani da fasahar don saukaka harkokin gudanar da gwamnati.
Matasan shida ‘yan Senegal da suka kafa kamfanin su ne; Abdoulaye Niasse da Moussa Mbaye da Cheikh Cissé da Fatima Fall Ndiaye da El hadj Samba Niang da Aminatou Djiri Diallo.
Ga misali a rayuwar kowane dan kasar Senegal, matakin aure wani babban mataki ne. Rashin fayyace wannan mataki yakan kawo cikas ga mutum wajen samun damar morar ayyukan gwamnati da suka shafi ilimi da lafiya da harkar banki.
Abin da wadannan matasan suke burin samarwa shi ne “a samu duka bayanan mutane kammale cikin lambar sirri ta QR,” kamar yadda El Hadj Samba Niang ya fada.
A bangarensa, Cheikh Cisse ya bayyana cewa “wannan fasahar ta QR za ta samar da dumbin bayanai, kamar su bayanan tarihin rayuwar mutum wato CV, da matakin aure, hada da shedar haihuwa da aure da mutuwa, da fayil din bayanan lafiya, da sauransu.
Ta hanyar yin sikanin kadai, lambar QR za ta fitar da ranar aurenka da kuma duk sauran bayanai masu alaka.
Ya batun tsaro da tsare sirri?
Muna rayuwa ne a duniya mai yawan sauyawa, wadda ke sa hanyoyin mayar da samar da ayyuka zuwa dijital.
Sai dai kuma, wannan cigaba yakan zo da kalubale manya-manya da suka hada da batun tsare sirrin mutane daga masu kutse, da kuma sauran nau’ukan satar bayanai.
Abdoulaye da abokan aikinsa suna sane da cewa, “bayanan sirri na mutum suna cikin hadari”.
Haka nan, irin tsarin da suka kirkiro zai iya zama abin da masu kutse za su kai wa hari. Kuma a fili yake satar bayanai yana da matukar illa.
Sai dai wadannan matasan masu zuba jari sun tabbatar mana da cewa sun samo hanyar gano masu aikin kutse.
Abdoulaye ya bayyana cewa, “Ku duba fa da lambar QR kacokam za a yi aikin! Kenan duk wanda ya iya mata kutse, zai cimma bayanan duka fayilolinka.
“Don haka, don samar da karin tsaro, muna aiki kullum don inganta tsaronmu da sabbin hanyoyin kulle bayanai, masu dauke da lambar QR kan kowane fayil.”
“Babu wani tsarin da ba shi da makasa, amma dai muna aiki don kare tsarinmu iya matukar iyawarmu, - don kare shi daga duk wani hadarin kutse ta kwamfuta”.
Tattalin lokaci da kuma kudi
Gwamnatin Senegal tana aiki don mayar da harkokin gudanar da gwamnati zuwa dijital.
Wannan sabon salo, a cewar masu aikin kafa shi, zai ba da damar tattalin kudi da lokaci ga mutanen kasar, a kokarinsu na samun takardu daga gwamnati.
Samun shaidar haihuwa, da shaidar ayyukan laifi, ko shaidar aure, duk suna da sauki a wasu kasashe. Amma a Senegal, kafin ka samu satifiket din haihuwa kawai, sai ka tafi ofishin hukuma sannan ka yi rijista.
Mutane da dama suna yin tafiyar daruruwan kilomita don samun takardun da suke bukata kafin su nemi aiki ko su shiga wata gasa, da sauran abubuwa.
Shi kuwa Niang, ya dage ne kan cewa lambar QR za ta saukaka rayuwa ga mutane, kamar yadda kuma za ta taimaka musu wajen tattalin lokaci da kudi.
Ya kara da cewa, “Alal misala, wani wanda aka haifa a Tambacounda (birni mafi girma a gabashin Senegal), zai iya yin sikanin din lambar QR mai dauke da bayanansa, domin ya samu duka takardun da yake bukata, ba tare da ya je ko ina ba.
“Daga nan, za a iya tura takardun kan lokaci. Babu bukatar yin wani kiran waya. Hakika duka matakan za a gudanar da su ne tare da sahalewar mutumin da abin ya shafa, saboda ba za mu yi sikanin bayanan mutum ba, in ba da amincewarsa ba.”
Wannan kamfani yana neman wata hanyar da zai hada gwiwa da ofisoshin gwamnati a Senegal, don ya kaddamar da wannan tsari.
Wannan tsari ba wai kawai zai saukaka ko rage cikowa a ofisoshi ba ne, zai kuma sassauta matakai ga mutanen da ke shan wahala wajen samun wasu takardu daga gwamnati.
“Yayin da kake neman takardar shaidar haihuwarka cikin gaggawa, kawai za ka bukaci shiga manhajar. Tun da akwai hadin gwiwa da ofishin gwamnatin, mutum zai iya sauke fayil dinsa sannan ya sabunta shi ko da yaushe yake bukata”.
Wannan wani gamammen shiri ne na ayyukan da sabon kamfanin yake samarwa ta hanyar samar da dama tabbatacciya, yayin da kamfanin kuma zai samu kudin shiga ta biyan kudi online.
Kuma yana samar da ayyuka a wasu fannonin kamar: lafiya da ilimi da sufuri.
Alal misali, Niasse ya ce, “Idan direba ya manta da takardun motarsa, zai iya nuna lambarsa ta QR ga jami’in hanya, wanda shi kuma zai yi sikanin dinta, ya duba takardun.”
Shi kuma Niang ya kara da cewa, “Tare da Lambar QR, ba ka bukatar ka damu da batar da shaidarka ta kammala difloma ko satifiket. Babu bukatar yin wata wahalar da a yanzu kake yi kafin samun wani kwafin satifiket. Tare da tsarinmu, za ka iya saukar da kwafin dijital na diflomarka daga intanet.”
A fahimtarsa, ta amfani da lambar QR kawai, likitoci za su iya samun satifiket din haihuwar jariri, kuma su iya gano ko jaririn ya samu adadin rigakafin da ya kamata.
Mafitar da ta dace
Kamfanin Art'Beau-Rescence yana da burin zama kamfani mai kulawa da lafiyar muhalli.
Tabbas, ana buga takardu na zahiri yayin harkokin gudanarwar gwamnati, kuma kasancewar ana yin takarda ne daga itatuwa da ake sarewa, hakan zai iya cutar da muhalli.
Ta amfani da tsarin lambar QR a ayyukan gwamnati, za a iya samun mafita kan kare muhalli a wannan yanayi.
Har ila yau, Niasse ya bayyana cewa, “Babban muradin shi ne a koma tsarin ‘green’ na kare muhalli, saboda muhimmancin muhalli.
"Kenan burin shi ne a mayar da duka harkoki zuwa dijital, don ya zamanto ba ma bukatar mu buga a takarda. Wannan ne dalilin muhimmancin komawa dijital.”
Niasse ya kuma kara da cewa, “Za mu iya inganta ayyuka ta hanyar maimaita amfani da kayan robobi don yin zoben rike makullai, wadda ke dauke da lambar QR da aka buga a kansa, ta amfani da fasahar 3D”.
Don gina wannan fasaha, Art'Beau-Rescence ya hada hannu da abokan aiki daga kamfanoni masu zaman kansu, a kokarinsu na janyo hankalin gwamnati, da ofisoshin gwamnati, wajen samar da hanyar samar da takardu cikin sauri.