Shin kuna fuskantar tashin farashin siminti a yankunanku? Hukumar Kula da Gogayyar Kasuwanci da Kare Haƙƙin Masu Sayayya ta Nijeriya (FCCPC) ta ce binciken da take yi a kasuwar simintin Nijeriya ya nuna yiwuwar samun aringizon farashi a ɓangaren.
A yanzu haka, hukumar tana binciken ko farashin da masu amfani da simintin ke biya ya dace da halin da kasuwa take ciki.
