| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Matatar Dangote ta samar da litar fetur 32.02 ga Nijeriya a Disamban 2025, in ji NMDPRA
Wata takardar bayanai da Hukumar Kula da Harkokin Sarrafawa da Tacewa da Sufurin Man Fetur a Nijeriya ta fitar ta ce Matatar Dangote ta samar da lita miliyan 32.02 na man fetur a watan Disamba.
Matatar Dangote ta samar da litar fetur 32.02 ga Nijeriya a Disamban 2025, in ji NMDPRA
Matatar Dangote / Reuters
10 awanni baya

Wata takardar bayanai da Hukumar Kula da Harkokin Sarrafawa da Tacewa da Sufurin Man Fetur a Nijeriya (NMDPRA) ta fitar ta bayyana cewa Matatar Dangote ta samar da lita miliyan 32.02 na man fetur a watan Disamba.

Takardar ta ce kamfanin ya nuna ƙarfin aiki mai kyau a watan Disamba, inda ya kai matsakaicin kaso, wato kaso 71 cikin 100 na amfani da ƙarfin matatar, daga cikin lita miliyan 50 da ya sanya a matsayin burinsa.

Takardar ta kuma yi ƙarin haske kan cewa ana ayyukan tace fetur a matatun man fetur guda uku na Kamfanin Man Fetur na Ƙasa na Nijeriya (NNPCL), duk da cewa matatun suna rufe.

Sai dai ta ce an fitar da dizal da aka riga aka samar a Matatar Fatakwal tun lokacin da take aiki kafin ranar 24 ga Mayun 2025, inda aka rinƙa samar da aƙalla lita 247,000 a rana.

Ta ƙara da cewa saboda lokacin bukukuwa, NNPCL da sauran kamfanoni sun shigo da lita miliyan 42.2 na man fetur a kowace rana domin cike gibin lita miliyan 72.4 na PMS da aka samar wa kasuwar cikin gida.

Har ila yau, takardar ta ce an ba da lasisi guda ɗaya don gina sabuwar matatar mai, yayin da Waltersmith (Train 2) mai ƙarfin ganga 5,000 a rana ta kammala shirye-shirye kinda ake shirin fara tace mai a Janairun 2026.