

Buhari Sale Abubakar, shi ne mai shafin Lugude da ke wallafa tsofaffin hotunan tarihi na Nijeriya, musamman na arewaci a shafukan sada zumunta.


Fitaccen ɗan Kannywood Yakubu Muhammad na fina-finai masu dogon zango irin su Garwashi da Labarina da Gidan Sarauta, ya ce zai iya auren irin Samira ta shirin Garwashi.


Farfesa Nasir Hasan Wagini na Jami'ar Umar Musa Yar'adua ya haɗa aikin koyarwa a jami'a da sana'ar da wasu ke gani a matsayin ƙasƙantacciya, wato sayar da kayan miya da hatsi.


Rabon abincin buɗe-baki da ake yi da azumi a fadin duniya yana kawo farin ciki ga masu azumi marasa hali, kamar yadda hakan ta faru a Abuja, babban birnin Nijeriya.


Wata matashiya ta samu kanta a cikin yanayin matsananciyar ƙiba, inda ta ringa fama da rashin lafiya saboda tsabar ƙiba, sannan ga tsangwama daga mutane.











































































