Zanga-Zangar adawa da yaƙi da mamayar Isra'ila a Gaza - ko zanga-zangar Dalibai ta Bazara - ta yaɗu a manyan kwaleji bayan kama masu zanga-zanga a Jami'ar Columbia a wannan watan.
Dalibai na kiran jami'o'in Amurka da su yanke hulda da kamfanonin da ke da alaƙa da kamfanonin da ke goyon bayan mamayar da Isra'ila ke yi a Gaza - wasu lokutan ma suna neman da a yanke alakar da Isra'ila baki daya.
Adadin wadanda aka kama a fadin kasar ya kai mutum 1,000 tun bayan da 'yan sanda suka kama masu zanga-zanga a Columbia a 18 ga Afrilu.
Kungiyoyin dalibai da dama ne suke shirya zanga-zangar a jami'o'in daban-daban. Kungiyoyin na aiki bia radin kansu, duk da dalibai na cewar abokansu da ke wasu makarantun ne ke karfafa musu gwiwa.
Ga dai yadda zanga-zangar ke ci gaba a Jami'o'in Amurka:
Jami'ar Columbia
Masu zanga-zanga a Jami'ar Columbia ne ne suka rikita makarantar wadda na ne cibiyar zanga-zangar goyon baya ga Falasdin, tuni makarantun Amurka suka fara dakatar da daliban da suka bijirewa wa'adin barin wuraren da suke yin zanga-zangar.
Mahukuntan kasaitacciyar Jami'ar da ke New York sun bukaci cewa a tashi a daina zanga-zangar, kowa ya watse ya zuwa karfe 2:00pm, ko kuma dalibai su fuskanci matakin ladabtarwa.
"Wadannan dabarun murkushewar ba wani abu ba ne idan aka kwatanta da kashe Falasdinawa 34,000," in ji sanarwar da daliban suka fitar a wajen taron bayan wa'adin da aka ba su na su watse ya kare.
"Ba za mu tafi ba har sai Columbia ta biya buƙatunmu... ko kuma a kore mu ta ƙarfi da yaji," in ji wani dalibi da bai bayyana sunansa ba.
Awanni kadan baya, mataimakin shugaban sadarwa na Jami'ar Columbia Ben Chang ya ce "Jami'ar ta fara dakatar da dalibai a matsayin wani bangare na kokarin tabbatar da tsaro a makarantunsu da za su dauka."
Shugaban Jami'ar Columbia Minouche Shafik ya fuskanci babbar suka daga tsangaya a ranar Juma'a amma duk da haka ya samu goyon bayan kwamitin amintattu, wadand asuke da karfin iko dauk da korar shugaban makarantar.
Wannan zanga-zanga ita ce ta baya-bayan nan a ala'adar Columbia mai tarihin sama da shekaru 50 - irin wadda ke taimaka wa karfafa gwiwar yaki da nuna fifikon farar fata a 1980, zanga-zangar yakin Iraki, da ma wasu da yawa.
Jami'ar Columbia ta dakatar da Soph Askanase, Bayahude mai zanga-zangar goyon bayan Falasdinm bayan an kama shi da zargin keta ka'ida.
"Rashin jin dadi ya bambanta da rashin samun tsaro," in ji Askanase. "Muna rayuwa a kasa, muna zuwa jami'ar da ke bayar da girmamawa sosai ga 'yancin fadin albarkacin baki, tattaunawa da muhawara."
Kame a Jami'ar Texas
A gefe guda, A Jami'ar Texas da ke Austin, 'yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zanga tare da kama da yawa daga cikin su, inda suka dinga lalata tantunansu, suna masu kari akan sama da mutum 50 da aka kama a fadin Amurka a karshen mako.
"Ba za a bayar da izinin gangami ba," in ji Gwamnan texas greg Abbott, a wani saƙo ta shafin sada zumunta a ranar Litinin.
"Maimakon haka, ana cafke mutane."
Zanga-zangar adawa da yaƙi a Gaza, da yadda aka kashe Falasdinawa fararen hula da dama, na zama kalubale ga jagororin makarantun.
A makon da ya gabata, daruruwan 'yan sanda - wasu a kan dawaki dauke da kulake - sun kutsa cikin masu zanga-zanga a jami'ar, suna tarwatsa su.
Jami'ar Northeastern
'Yan sanda a wajen zanga-zanga sun lalata matsugunan mutanen a Jami'ar Notheastern da ke Boston a ranar Asabar.
'Yan sandan jiha sun bayyana cewa kusan masu zanga-zanga 1000 aka kama kuma za a tuhume su da laifukan leka gine-gine da nuna rashin da'a.
Jami'ar Northeastern ta bayyana cewa "an samu kwararru sun shiga znaga-zangar" wadanda ba su da alaka da jami'ar sanna ana nuna kyamatar Yahudawa ciki har da kalaman "kashe Yahudawa".
Amma masu zanga-zangar kubutar da Falasdinu sun bayyana cewa, wadanda suke kalubalantarsu ne ke da alhakin yin kalamai munana, "kuma babu wani dalibi da ya maimaita munanan kalaman."
Jami'ar Mary Washington
Gwamman mutane, ciki har da dalibai tara ne aka kama a ranar Asabar bayan zanga-zanga a jami'ar Mary Washington da ke Fredricksburg, Virginia, kamar yadda sanarwar da shugaban jami'ar ya fitar ta bayyana.
An bayyanawa mahalarta a ranar Juma'a cewa za su iya zama idan suka bu dokokin jami'ar, sannan an sanar da karin ka'idojin zama lafiya ga masu shirya gangamin.
An hana taruwar jama'a waje guda, an hana kafa tantuna. An lalata tantunan a daren Juma'a, kuma an ci gaba da zanga-zangar zuwa ranar Asabar a lokacin da aka kora su baya.
A yammacin ranar Asabar kuma, an fada wa mahalartan zanga-zangar da su bar wajen, kamar yadda sanarwar shugaban ta bayyana. Bayan wani dan lokaci, mutane 16 da ke zaune a Dandalin Jefferson sun shiga hannun 'yan sanda saboda aikata laifin shiga gine-gine ba tare da izini ba.
Jami'ar Southern California
A ranar Asabar Jami'ar Southern California ta rufe gininta na Park na wucin gadi ga wadanda ba 'yan asalin yankin ba, ba tare da bayar da dalilin rufewa ko daukar matakin ba.
Joel Curran, babban jami'in yada labarai ya ce masu zanga-zangar sun lalata kayan USC "wannan zama na ci gaba da zama wanda ba halastacce ba a jami'armu", sannan suna hantara da cusgunawa daliai da sauran ayyuka.
Dalibai sun ƙi amincewa da ganawa da shugaban kamarantar Carol Folt, kuma hukumar gudanarwar na fatan mayar da martani yadda ya kamata, in ji Curran.
Jami'ar ta soke bikin yaye daliban d ata shirya gudanarwa a ranar 10 ga Mayu. Ta kuma soke bayanin da mai gyon bayan falasdin zai yi, tana mai bayyana dalilai na tsaro.
Ofishin 'yan sandan Los Angeles ya ce an kama sama da mutane 90 a ranar Larabawa a lokacin zanga-zanga a Jami'ar.
Jami'ar California, Los Angeles
Masu zanga-zanga sun dinga ihu a lokacin zanga-zangar a ranar Lahadi a Jami'ar California, Los Angeles.
'Yan sanda sun tare hanya kafin daruruwan mutanen sun hadu da babban taron jama'a a lafin Dickson, kusa da wajen da daliban da ke goyon bayan falasdin suke zaune a cikin tantuna.
Masu zanga-zangar kalubalantar wadannan kuma sun yi tasu da taken "Goyon Bayan Dalibai Yahudawa" inda suke ce manufarsu ita ce "kalubalantar kalaman nuna ƙyama da ƙyamatar Yahudawa".
Jami'ar George Washington
Kusan dalibai 50 na Jami'ar George Washington a birnin Washington DC, sun kafa sansani a harabar makarantar a ranar Alhamis.
Rukunin daliban da farfesoshi sun gudanar da nasu tattakin tare da haduwa da su.
Masu zanga-zangar na bukatar cewa lallai jami'ar ta janye dakatarwar da ta yi wa wasu dalibai da ke nuna goyon bayan Falasdinawa.
A wata sanarwa da jami'ar ta fitar ta bayyana cewa masu zanga-zangar da ke kula da jami'ar sun karya ka'idar shiga harabarta tare da kafa sansanin.
An saka gudanar da azuzuwan karshe a ranar Litinin, sannan a dawo karatu a ranar 19 ga Mayu.
Sakamakon hayaniyar da masu zanga-zangar ke yi, jami'ar ta ce za ta mayar da daliban ajin karshe na sashen nazarin shari'a zuwa wani ginin maimakon wanda suke.
Virginia Tech
Kakakin jami'ar a ranar Litinin ya bayyana cewa an kama wasu da ba a bayyana su nawa ba ne sakamakon zanga-zanga a jami'ar Virginia da ke Blacksburg.
Masu zanga-zangar sun fara mamaye bangaren masu karatun digirgir a ranar Juma'a, in ji sanarwar da jami'ar ta fitar.
Taron jama'ar ya saba wa dokokin makarantar, in ji jami'ar, amma kuma wajen na da nutsuwa da zaman lafiya sama da yadda yake a karshen mako.
Bayan masu anga-zangar sun yi kokarin mamaye wajen gaba daya tare da cibiyar dalibai a ranar Lahadi, "sai wajen ya zama cikin rashin tsaro", aka kuma shawarci wadanda suka taru da su bar wajen.
An yi gargadin za a tuhumi wadanda suka gaza aiki da umarnin.
Jami'ar Jiha ta Fasaha ta California da ke Humboldt
Mahukuntar jami'ar sun kara wa'adin rufe ta zuwa 10 ga Mayu - karshen zangon karatu - tana mai cewa za a ci gaba da bayar da umarni daga nesa saboda yadda masu zanga-zangar a Jami'ar da ke Arewacin California suka yi amfani da kujeru da tantuna wajen toshe hanyr shiga a ranar 22 ga Afrilu.
An sanar da za a dawo makarantar a ranar 11 ga Mayu.
Jami'ar Case Western Reserve
An kama sama da mutane 20 sannan aka sake su jim kadan bayan an kwashe tantunan da suka kafa inda suka bar wajen a ranar Litinin a Jami'ar Jami'ar Case Western Reserve da ke Cleveland.
Masu zanga-zangar sun kafa sansanoni a wuraren da jama'a ke zama inda suka kafa wani allo da aka rubuta "Barka da Zuwa Jami'ar Jama'ar Falasdin" inda suka yi kira ga makarantar da ta kauracewa Isra'ila.
Nan da nan 'yan sanda suka je tare da lalata tantunan. An saki wadanda aka kama ba da jimawa ba, kuma ba a bayyana ko za a tuhume su da aikata wani babban laifi ba.
Jami'ar Yale
Masu zanga-zanga a jami'ar Yale sun kafa sabon sansani da gwamman tantuna a ranar Lahadi, kusan mako guda bayan 'yan sanda sun lalata sansanoni irin wadannan.
Masu zanga-zanga da jami'an makarantar sun ce shugabannin Yale sun sanar da su cewa za su fuskanci ukuba, ciki har da dakatarwa da yiwuwar dauri.
Ba a fadi ranar bari ba, in ji Yale a wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin da ke cewa suna goyon bayan zanga-zangar lumana da neman 'yancin bayyana ra'ayi, amma ba za su lamunci goyon bayan karya manufofi ba.
Jami'an makarantar sun ce ana zanga-zangar a kusa da gidajen dalibai, wuraren da suke zama su yi karatun jarrabawar karshe, kuma dole a bayar da dama ga kungiyoyi su gudanar da taruka.
Jami'ar North Carolina da ke Chapel Hill
A ranar Litinin, gwamman mutane da ba sa aikin komai ne suka taru tare d kfa sansani a sun zanga-zanga a Jami'ar North Carolina da ke Chapel Hill.
Dalibai da sauran ma'aikatan jami'a, sun kwanta da barguna suna rera waka a yayinda wasu suka zagaye wata mace da ke rawa a kaffaya, wani nau'in hijabi na matan Larabawa.
An kafa tantuna a ranar Lahadi inda aka yi tattakin neman jami'ar da ta kaurace wa Isra'ila.
Daliban Jami'ar Washington a reshen jami'ar d ke Seattle sun kafa sansani su ma a ranar Litinin a gaban babban dakin taro na Miller.
Kusan tantuna shida ake iya gani a filin mai ciyayi, duk da allon da ke cewa "ba yar da da zaman dabaro ba".
Gwamman masu zanga-zangar sun makala tutocinsu a jikin tantunan da ke dauke da rubutun nuna goyon baya ga gaza. Suna neman jami'ar ta yanke hulda da Boeing. wanda aka samar a Seattle, kuma yake amfani kayan da Dakarun Tsaron Isra'ila ke amfani da su, sannan ta dakatar da duk wani karatu da ake zuwa a yi a Isra'ila.