Daraktan Sadarwa na Turkiyya ya ziyarci baje-kolin zane-zane na yara masu zane daga Gaza, a wajen taron Diflomasiyya na Antalya Diplomacy Forum (ADF), inda ya ce manufar yaran ita ce nuna tsarin Isra'ila na yaɗa "ƙarairayi".
Ranar Juma'a, Fahrettin Altun ya ziyarci bikin da aka sanya wa suna "Bulletproof Dreams: Gaza Child Artists Exhibition", wanda Ma'aikatar Sadarwa ta Turkiyya ta shirya.
Ya ce an ƙaddamar da taron ADF a matsayin taron diflomasiyya mafi muhimmanci a Turkiyya, wanda ya karɓi baƙuncin shugabannin duniya da dama.
Ya ƙara da cewa, "A wannan taron, muna so mu bayyana batun Gaza, wanda shi ne wani babban ciwo da ke damun duniya a wannan lokaci, don baƙinmu daga duniya da suka zo nan da manufar kawo ci-gaba."
Ya kuma ce, "Shugaba Recep Tayyip Erdogan ne zai buɗe bikin nune-nunen da yara masu basira daga Gaza suka yi, inda Shugaban da wasu shugabannin duniya za su gabatar da jawabansu a taron bayan sun wuce ta zauren nune-nunen."
Daraktan Ma'aikatar Sadarwar ya yi nuni kan cewa nune-nunen suna bayyana irin "mummunan zaluncin" da Isra'ila ta aikata a harin Operation Cast Lead na 2009.
Ya bayyana cewa, "Wadannan zane-zanen a zahiri suna nuna yadda zaluncin Isra'ila yake daɗadɗe".
"Idan ka kalli nune-nunen, wanda har yanzu a buɗe suke yau a nan da kuma a Taksim (Istanbul), za ka gani a bayyane cewa abin takaici ne Isra'ila ta yi amfani da bam mai sinadarin phosphorus a wannan ranar, sun kai hari kan farar hula, sun kashe yara da mata da ma'aikatan lafiya."
"Kuma har yau suna ci gaba da wannan kisan gillar."
Buƙatar haɗin-kan duniya
Altun ya jajanta cewa yara sun ga wannan kisan gillan da idanunsu, inda yake cewa: "A bayyane yake ƙarara, yara sun sanar da hakan ta hanyar zane-zanensu".
"Tabbas mun yi kokari mu nuna wannan a baje-kolin nune-nunen ta allunan dijital da fasahar zamani. A nan muna so mu nuna wa duniya tsabagen zaluncin da ake yi a Gaza, mu nuna shi a zahiri ta mahangar yara".
Ya kuma ce, "Ta wannan hanya, muna so mu bayyana cuzgunawar da ake yi, sannan a wani ɓangaren mu nuna yadda Turkiyya ke fafutuka kan kawar da wannan zaluncin a faɗin duniya, da ganin bai ƙara faruwa ba."
Daraktan ya jaddada cewa, don ganin an hana wannan zaluncin faruwa, ya wajaba ga duka duniya ta hada kai da yin fafutuka kan tsayar da gaskiya da adalci.
"Manufar wannan baje-kolin nune-nunen shi ne fito da tsarin Isra'ila na ƙarairayi a fili".