Wata mata 'yar Iraqi riƙe da hoton Shugaban Hezbollah Hassan Nasrallah a Baghdad Iraƙi, yayin da take halartar tattaki bayan sanarwar mutuwarsa, ranar 28 ga Satumba, 2024. / Hoto: Reuters  

Shugabannin duniya sun yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar mummunan martani bayan ƙungiyar Hezbollah ta Iran ta sanar da kashe shugabanta da ya shafe dogon lokaci, a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai wata unguwa da ke bayan garin Beirut

Kisan shugaban ƙungiyar ya ƙara tsoron da ake da shi na ɓarkewar gagarumin yaƙi a Gabas ta Tsakiya.

Majalisar Ɗinkin Duniya

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya ce ya "damu sosai kan yadda rikicin da ake yi yake ƙara ƙazancewa a Beirut cikin sa'o'i 24".

Turkiyya

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya wallafa a shafin X cewa an jefa Lebanon cikin "kisan kiyashi", sai dai ba tare da ya ambaci Nasrallah ba kai-tsaye.

Saudi Arabia

Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Faisal bin Farhan Al Saud ya shaida wa Majalisar Ɗinkin Duniya cewa "wannan ƙazancewar za ta yi... mummunan tasiri a gaba ɗayan yankin.

"Muna kira ga duka ɓangarori su nuna dattaku da kai zuciya nesa, don kaucewa ɓarkewar cikakken yaƙi a yankin."

Iran

Mataimakin Shugaban Iran Mohammad Reza Aref ya gargaɗi Isra'ila cewa mutuwar Nasrallah za ta "kawo rushewar su", kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Iran, ISNA ya ambato shi.

Ma'aikatar harkokin waje ta Iran, wadda ke samar da kuɗi da makamai ga Hezbollah, ta ce ayyukan Nasrallah za su ci gaba bayan rasuwarsa. "Tsarkakkiyar manufarsa za ta tabbata wajen 'yantar da birnin Quds, da yardar Allah," a cewar kakakin ma'aikatar, Nasser Kanani a wata wallafa ta X.

Shugaban addini na ƙasar Ali Khamenei ya ayyana kwanaki biyar na makoki a ƙasar.

Hamas

Ƙungiyar Hamas ta kira kisan Nasrallah a matsayin "harin ta'addanci abin ƙyama".

Gwamnatin Falasɗinu

Shugaban Falasɗinu Mahmud Abbas ya ayyana "matuƙar jajantawarsa" ga Lebanon kan mutuwar Nasrallah da ta farar hula, waɗanda "suka mutu sakamakon tsabagen zaluncin Isra'ila", cewar wata sanarwa daga ofishinsa.

'Yan Houthi

'Yan Houthi a Yemen, waɗanda suke harba makamai kan jiragen ruwa a tekun Maliya don mara wa Hamas baya, sun faɗa a wata sanrwa cewa kisan Nasrallah "zai ƙara watar sadaukarwa, da zafin kishi, da ƙarfinmu" kan Isra'ila, kuma shugabansu ya sha alwashin cewa kisan Nasrallah "ba zai tafi a banza ba".

Rasha

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce "muna ƙarfafa yin tir da wannan kisan na siyasa da Isra'ila ta yi" kuma ta nemi a "gaggauta tsagaita wutar soji" a Lebanon.

Isra'ila za ta ɗauki "cikakken alhaki" kan wannan "mummunan" sakamakon da kisan zai haifar a yankin, a cewar wata sanarwar ma'aikatar.

China

China ta ce "ta yi matuƙar damuwa" kuma "tana lura da" tashin hankalin da ke ƙazanta a Gabas ta Tsakiya, bayan Isra'ila ta kashe shugaban Hezbollah.

"China tana bibiyar lamarin kuma ta damu matuƙa da ƙazancewar lamura a yankin," cewar ma'aikatar harkokin waje a wata sanarwa, kuma ta nemi "duka ɓangarori musamman Isra'ila su ɗauki matakai nan-take don saukar da ƙurar."

Amurka

Shugaba Biden ya ce mutuwar Nasrallah "wani mataki ne na adalci kan waɗanda ya zalunta, ciki har da dubban Amurkawa da 'yan Isra'ila da 'yan Lebanon farar hula".

Gwamnatin Amurka na mara wa 'yancin Isra'ila baya na kare kanta daga "ƙungiyoyin ta'adda da Iran ke goyon baya" kuma za a "inganta taimakon tsaro" daga dakarun Amurka a yankin za a faɗaɗa shi, kamar yadda Biden ya faɗa a wata sanarwa.

Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris ta ce Nasrallah "ɗan ta'adda ne wanda ke da jinin Amurkawa a hannunsa" kuma ta ce za ta "goyi bayan Isra'ila a koyaushe kan 'yancinta na kare kanta daga ƙungiyoyin ta'adda da Iran ke goyon baya kamar Hezbollah, Hamas, da 'yan Houthi."

Jamus

Ministar Harkokin Waje ta Jamus Annalena Baerbock ta faɗa wa gidan talabijin na ARD cewa kisan "yana barazanar wargaza zaman lafiyar duka Lebanon", wadda "ba zai yi kyau ga tsaron Isra'ila ba".

Canada

Firmanistan Canada Justin Trudeau ya bayyana Nasrallah a matsayin "shugaban ƙungiyar ta'addanci da ta kai hare-hare da kashe farar-hula, kuma ta haifar da mummunar damuwa a yankin".

Amma ya yi kra da a saka ƙaimi don kare farar hula a rikicin, kuma ya ƙara da cewa: "Muna kiran a kwantar da hankula a wannan yanayi mai tsanani."

Birtaniya

Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy ya faɗa a wata wallafa a X cewa ya yi magana da Firimiyan Lebanon.

"Mun cim ma cewa akwai buƙatar tsagaita wuta nan-take don kawo ƙarshen zubar da jini. Maslahar diflomasiyya ita ce kawai hanyar maido da tsaro da zaman lafiya ga al'ummomin Lebanon da Isra'ila," in ji shi.

Faransa

Ministan harkokin waje na Faransa Jean-Noel Barrot ya nemi Isra'ila "ta dakatar da hare-harenta a Lebanon nan-take", kuma ya ce ƙasarsa na adawa da duk wata mamaya ta ƙasa cikin Lebanon.

Faransa kuma ta ce "muna kira da sauran masu hannu a batun, musamman Hezbollah da Iran, su ƙauracewa duk wani mataki da zai haifar da ƙarin rikici a yankin da yaƙi", cewar sanarwar ma'aikatar harkokin wajen.

Cuba

A wata wallafa a X, Shugaban Cuba Miguel Diaz-Canel ya kira kisan "mummunan kisan gilla" wanda ya "ke barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin da na duniya, wanda Isra'ila ke da cikakken alhaki tare da hannun Amurka."

Argentina

Shugaban Argentina Javier Milei ya wallafa saƙo a X daga wani mamban majalisar mashwartansa na tattalin arziƙi, David Epstein, wanda ya yaba wa kisan.

"Isra'ila ta kawar da ɗaya ciki manyan masu kisa a yau. Yana da alhakin hare-hare a #ARG," in ji shi. "Yau duniya ta samu wani ɗan 'yanci".

Venezuela

Shugaban Venezuelan Nicolas Maduro ya bayyana goyon baya ga Nasrallah da Lebanon.

"Suna so su halasta kisan, amma wajen halaka shi sun kai hari kan gine-gine sun kashe ɗaruruwan mutane. Kalma ɗaya ce ta dace da wannan: laifi."

TRT World