0843 GMT — Ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce majalisar ministocinsa ba za ta yi taro don amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ba, yana mai zargin kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas da haifar da "rikici a ƙurarren lokaci".
Ba tare da yin karin haske ba, ofishin Netanyahu ya zargi Hamas da yin watsi da wasu sassan yarjejeniyar a wani yunƙuri na "karɓar rangwame a minti na ƙarshe".
Majalisar zartarwar Isra'ila ta shirya amincewa da yarjejeniyar ranar Alhamis.
0607 GMT — Isra'ila ta kai hari kan fararen hula bayan cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta
Duk da sanarwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta, sojojin Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a Zirin Gaza, lamarin da ya janyo asarar rayukan fararen hula.
Wasu shaidun sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa wani jirgi mara matuki na Isra'ila ya kai hari kan tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu a yammacin birnin Deir al Balah da ke tsakiyar Gaza, lamarin da ya haddasa jikkata mutane da dama ciki har da yara.
Hukumomin lafiya har yanzu ba su ce komai ba kan lamarin ko kuma bayyana adadin wadanda suka jikkata.
Shaidu sun kara da cewa, jami’an kare farar hula da sauran jama'a sun garzaya wurin da lamarin ya faru domin kashe gobarar da ta tashi a cikin tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu.
0346 GMT — Shugaban Brazil Lula ya jinjina wa yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza da Isra'ila
Shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya yi maraba da labarin yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas ta Falasdinu yayin da take ci gaba da mara baya ga samar da kasashe biyu.
Lula ya yaba da labarin a shafinsa na X yayin da ya bayyana bukatar bangarorin biyu su tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya.
"Bayan tsananin wahala da barna, labarin cewa a karshe an cim ma matsaya kan tsagaita bude wuta a Gaza ya kawo kyakkyawar fata, da fatan kawo karshen rikicin da kuma sako mutanen da aka yi garkuwa da su, su taimaka wajen samar da mafita mai ɗorewa da za ta samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya baki ɗaya." "in ji shi.