Dubbban ɗaruruwan Iraniyawa sun taru domin makokin mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi da mutane bakwai da ke cikin tawagarsa, waɗanda suka mutu a haɗarin helikwafta a wani waje mai tsaunuka a arewa maso yammacin ƙasar.
Yayin da wasunsu ke ɗaga tutar Iran da hotunan shugaban a ranar Alhamis, masu makokin sun fara tattaki daga Dandalin Tsakiya a birnin Tibriz da ke arewa maso yamma, inda nan ne Raisi ya nufa lokacin da helikwaftan nasa ya faɗo ranar Lahadi.
Sun ringa tattaki a bayan wata babbar mota wacce ke ɗauke da gawar Raisi da sauran mataimakan nasa bawaki.
An daina jin ɗuriyar helikwaftan nasu lokacin da yake hanyar komawa Tibriz bayan Raisi ya halarci ƙaddamar da wani aikin haɗin gwiwa a kogin Araz, wanda yake wani ɓangare na iyakar Iran da Azarbaijan, a wani biki tare da takwaransa Ilham Aliyev.
An ƙaddamar da wani gagarumin aikin ceto ranar Lahadi yayin da sauran jirage biyu da suke tafiya tare da jirgin Raisi suka neme shi suka rasa, sannan suka daina jin ɗuriyarsa a cikin wani hali na rashin kyan yanayi.
Gidan Talabijin ɗin ƙasar ya sanar da mutuwar Raisi a cikin wani rahoto ranar Litinin, yana cewa Mai yi wa Ƙasar Iran Hidima, Ayatollah Ebrahim Raisi ya cimma mafi ɗaukakar shahada," ana nuna hotunansa yayin da ake karatun Alkur'ani.
Mutanen da suka mutu tare da shugaban na Iran sun haɗa da Ministan Harkokin Waje Hossein Amirabdollahian, da jami'an yanki da kuma wasu jami'an tsaronsa.
Babban Hafsan sojojin Iran Mohammad Baghari ya ba da umarnin gudanar da bincike kan dalilan hatsarin, yayin da Iraniyawa a birane a faɗin ƙasar suke makokin Raisi da 'yan tawagarsa.
Dubban mutane sun taru a Dandalin Valiasr dake babban birnin ƙasar ranar Litinin.