Wani jirgin ruwa ya samu lahani bayan da makamai masu linzami suka sauka kansa har sau biyu, gab da gaɓar tekun Yemen, sakamakon wani harin baya-bayan nan kan jiragen ruwa da ke safarar kaya a Bahar Maliya, wanda ƙungiyar Houthi ke ɗaukar alhaki.
Cibiyar tsaro ta Hukumar Kasuwancin Kan Teku ta Birtaniya, UKMTO, ta ce harin ya afku ne a kudu maso yammacin tashar ruwan Yemen ta Mokha, ranar Juma'a.
A harin farko, jirgin ya yi karo da "fashewa dab da jirgin, wanda ma'aikatan da ke kan jirgin suka ji", cewar UKMTO a shafin X.
"Hari na biyu kan jirgin ya ƙunshi abin da ake zargin makamai masu lizami ne guda biyu, waɗanda suka haifar da lahani."
'Yan awanni bayan nan, wani kamfanin tsaro na Birtaniya, Ambrey, shi ma ya ba da rahoton wani hari kusa da tashar bakin ruwa ta Mokha.
Ambrey ya ce, "Makamai masu linzami guda uku aka gani" a harin.
A cewar Ambrey, "Wani jirgin dakon mai ɗauke da tutar Panama shi ne jirgi mafi kusanci a wajen. Jirgin tankar a baya mallakin Birtaniya ne [amma]... mamallakansa sun sauya a Nuwamban 2023".
Sun ce a yanzu jirgin na da rijista a ƙasar Seychelles, kuma "yana tafiya ne daga Primorsk, a Rasha, zuwa Vadinar, a Indiya".
Daga baya, kakakin Houthi Yahya Saree, ya sanar da ɗaukar alhakin harin a wata wallafa a shafin X.
Ya ce "dakarun ruwa" na Houthi sun hari "jirgin dakon mai na Birtaniya [Andromeda Star] a Bahar Maliya, ta amfani da makamai yaƙin ruwa, kuma harin ya faɗa kan jirgin".
Rundunar Sojin Amurka ma ta tabbatar da harin kan Andromeda Star, da kuma kan wani jirgin daban mai suna MV Maisha.
A cewar rundunar CENTCOM ta Amurka a shafin X, mayaƙan Houthi sun harba makamai masu linzami na yaƙar jirgin ruwa guda uku, "a wajen da MV MAISHA yake", sannan da "MV Andromeda Star, wani jirgi mallakin Birtaniya mai ɗauke da tutar Panama, wanda ƙasar Seychelles ke aiki da shi".
Rahoton ya ƙara da cewa, "MV Andromeda Star ya ba da rahoton samun lahani ƙarami, amma yana ci gaba da tafiyarsa," kuma an ce babu wanda ya jikkata.
'Ƙarin ayyukan soji'
Harin baya-bayan nan ya zo bayan raguwar hare-hare daga 'yan Houthi na Yemen, wanda a baya sun kai harin gomman makamai masu linzami da jirage marsa matuƙi kan jiragen ruwa "masu alaƙa da Isra'ila ko da suka nufi Isra'ila", tun Nuwamba, don nuna goyon baya ga Falasɗinawa da ke fama da yaƙin Isra'ila a Gaza da aka yi wa mamaya.
Duk da raguwar hare-haren a makonnin baya, Houthi ta sanar a maraicen Laraba cewa, suna "ci gaba da ɗaukar matakan ayyukan soji kan duka abokan gaba a Bahar Maliya, da Tekun Arabia, da tekun India".
Tun da fari ranar Juma'a, Rundunar Sojin Amurka ta ce ƙawancen sojinta sun lalata jirage marasa matuƙi guda biyu a yankunan da Houthi ke jagoranta a Yemen, bayan sun harba makamai masu linzami zuwa tekun Aden.
Harin makamai masu linzamin da aka ƙaddamar ranar Alhamis sun hara, amma ba su faɗa kan jirgin dakon kaya mai ɗauke da tutar Liberia ba, mai suna MSC DARWIN VI, a cewar cibiyar sadarwa ta haɗaka.
Ƙungiyar Houthi ta ɗauki alhakin kai harin, inda suka zargi jirgin da kasancewa mallakin Isra'ila ne.
'Yan Houthis, wanɗanda suke iko da kaso mafi girma na gaɓar tekun Bahar Maliya a Yemen, suna cikin "da'irar tirjiya" wadda ta haɗa da ƙawayen Iran da ke kai hari kan Isra'ila saboda yaƙin da take a Gaza, inda gwamnatin Isra'ila ta kashe sama da Falasɗinawa 34,000 kuma suka jikkata wasu 80,000.
Masana da dama sun ce yaƙin tuni ya kai matakin kisan ƙare-dangi.