"Gazawar sojojin na yin aiki da dokokin aikinsu ya janyo sojoji na kashe fararen hula ba gaira ba dalili, kuma ba a hukunta su"

Sojojin Isra'ila sun samar da "yankunan mutuwa" a ciki da wajen Gaza da manufar kashe Falasɗinawa da suka taka ƙafarsu a wuraren, kamar yadda jaridar Haaretz ta ruwaito majiyoyin sojin na faɗa.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha yabon sojojin ƙasar da cewa "Sojoji mafi aiki da ƙa'idoji a duniya".

Sai dai kuma, dalilai da hujjojin da aka samu sun saɓa da kalaman nasa. Abubuwan da sojojin Isra'ila ke yi sun sa Amurkawa na sanya alamar tambaya kan biliyoyin dalolinsu na haraji da ake kashe wa sojojin Isra'ila suna cin zarafin Falasɗinawa.

A baya-bayan nan Amurka ta amince a aike da bama-bamai masu nauyin fam 2000 da ƙarin wasu makamai zuwa Isra'ila.

Duk da bayar da tabbaci daga gwamnatin Biden kan cewa za a yi amfani da makaman bisa dokokin ƙasashen duniya, rahoton binciken na jaridar Isra'ila ta Haaretz ya yi ƙarin haske kan asalin ayyukan da sojojin da Amurka ke ɗaukar nauyi suke yi a Gaza.

Wani jami'in ma'ajiyar kayayyakin soji da jaridar Haaratz rta ruwaito ya bayyana cewa "yankin yaƙi" na da muhimmanci a Gaza. Na nufin wani yanki da aka jibge sojoji, a gidajen da babu kowa, sannan aka bar shi babu alamun akwai sojoji a ciki. Wani sunan da ake sanya wa waɗannan wurare shi ne 'yankunan kisa'

Jami'in ya ƙara da cewa a kowanne yanki na kisa ko yaƙi, kwamandoji ne ke bayyana yadda za a yi aiki, yawancinsu na kawo dokokinsu na kansu.

Jami'in ya ce "Da zarar mutane sun shiga yankunan ana bayar da umarni a harbe su, ko da kuwa ba sa ɗauke da makami."

Kisa lokaci zuwa lokaci

Rahoton ya bayar da yanayi mai muhimmanci game da hotuna da bidiyon da jirgin Isra'ila mara matuki ya ɗauka, wanda ya aka watsa a tashar Aljazeera.

Bidiyon mara daɗin kallo ya nuna jirgin yaƙi mara matuƙi na Isra'ila na shawagi kan wasu maza Falasɗinawa da ba sa ɗauke da makamai, yana ta bin su har zuwa yankin Han Younu na kudancin Gaza. Daga baya an harba musu makami mai linzami inda aka kashe su.

"A bayyane take ƙarara cewa wannan na cikin jerin sunayen 'yan Hamas da aka kashe", in ji rahoton. Sai dai kuma, wani babban jami'in sojin Isra'ila da ya tattauna da Haaratz ya ce mutanen ba sa ɗauke da makamai, kuma ba sa yin wata barazana ga sojojin Isra'ila a yankin.

Jami'in ya ƙara da cewa babu tabbacin mutanen suna da hannu wajen kai harin makamin roka, ko kuma fararen-hula ne da ke neman abinci.

Kawai mutane ne da suke a kusa da wajen da aka kai harin - wataƙila farar-hula ne da ke neman abinci.

Adadin Falasɗinawan da Isra'ila ta kashe a Gaza ya haura mutum 33,000. Wannan bayani ne gaskiyar yadda ake yawan kashe Falasɗinawa a hare-haren kan mai-uwa-da-wabi da sojojin Isra'ila ke kaiwa Gaza.

Wani babban kwamanda ya yi nuni da cewa fararen-hula da dama a arewacin Gaza ba sa cikin yankunan da ake kaiwa agajin gaggawa, kuma sun zauna a gidajensu don kare su daga sata. Kuma waɗannan fararen-hula na cikin hatsari.

"Za su iya zama a cikin gine-ginen da ke kusa da matsugunin sojoji," in ji kwamandan.

Wani bidiyo da sashen Larabci na Aljazeera ya watsa ranar 27 ga Maris ya nuna sojojin Isra'ila na harbin wasu Falasɗinawa da ba sa ɗauke da makamai a Gaza, ɗaya daga cikinsu na ɗaga farin ƙyalle da ke nuna cewa suna ƙaunar zaman lafiya.

Wani wakilin Aljazeera ya ce maza na ƙoƙarin komawa gidajensu a arewacin Gaza ta hanyar al-Rasheed, hanya ɗaya kaɗai da ake iya bi, a lokacin da suka gamu da sojojin Isra'ila kusa da sha-tale-talen Nabulus, kudu maso-yammacin Gaza.

Bayan harbin, an tattara mutanen da wata buldozar sojoji, tare da binne su a cikin yashi da ɓaraguzai, a ƙoƙarin ɓoye shaidar kisan.

"Waɗannan abubuwa ne munana masu tayar da hankali saboda muna kallo ana kisan gilla," in ji Nebal Farsakh, kakakin Ƙungiyar Bayar da Agaji ta Falasɗinu ta Red Crescent, a tattaunawar da ya yi d Aljazeera.

"Isra'ila na ci gaba da cin karenta babu babbaka saboda shirun da ƙasashen duniya suka yi," in ji shi.

"Dubban Falasɗinawa nawa ne za a kashe kafin duniya ta ɗauki matakin da ya kamata na tuhumar Isra'ila kan ta'annatin da take yi sannan ta tsagaita wuta?"

Ba a aiki da dokokin yaƙi

A rahoton Haaretz, wani jami'i ya bayyana yadda wani mummunan al'amari ya afku a arewacin Gaza a lokacin da aka kai hari ta sama bayan an gano akwai fararen-hula a wajen.

"Wannan ya afku a wajen da ba shi da nisa daga yankin yaƙi inda akwai kasuwa da ta cika da jama'a, yara na wasa a kan kekuna, wata duniya ta daban," kamar yadda rahoton ya faɗa, inda shi kuma jami'in ya ce su ba su san akwai yara da fararen-hula a yankin ba.

Wani sojan na daban kuma ya faɗi irin umarnin da aka dinga ba su na su ci gaba da yin haka, ya ce an ba su umarnin su kashe duk wanda ya shiga yankunan da suke aiki.

"A wajen kwamandojinmu, idan muka gano wani a yankin da muke aiki wanda ba ya tare da rundunarmu, an ce mu harbe da kashe shi kawai," in ji shi. "An faɗa mana ƙarara cewa ko da mutum ya gudu cikin ginin da ke da mutane a ciki, to mu buɗe wa ginin wuta tare da kashe ɗan ta'addar, ko da za a raunata waɗanda suke cikin gidan."

A wata tattaunawa da sashen Ingilishi na Aljazeera, ɗan jarida kuma marubucin littafin "The Palestine Laboratory", Antony Loewenstein, ya yi ƙarin haske game a bambanci tsakanin ikirarin Isra'ila na aiki da dokokin yaƙi da kuma kalaman sojoji na cewa ana ba su wani umarni na daban a filin daga.

Ya ce gazawar sojojin na yin aiki da dokokin aikinsu ya janyo sojoji na kashe fararen-hula ba gaira ba dalili, kuma ba a hukunta su.

"Al'adar soja ita ce karbar umarni daga sama. Kana da Ministan Tsaro na Isra'ila da kuma wasu da dama a rundunar sojin Isra'ila tun 7 ga Oktoba da ke ta rarraba takardu ɗauke da bayanan yadda Isra'ila za ta kawo ƙarshen Falasɗinawa. Wannan al'ada ce ta kawo irin wannan kisan na gilla da rashin imani," in ji Loewenstein.

"Ba wai a jiya ko yau ba, a'a cikin shekaru da suka shuɗe, akwai sojojin Isra'ila da ke ta magana game da yadda babu wani hukunci ga waɗanda ke kashe Falasdinawa ko jikkata su, ba wai a Gaza kadai ba, har ma a Yammacin Gabar Kogin Jordan da Gabashin Ƙudus."

TRT World