'Yan'uwan Han Suofeiya ne suka yi wa gawarta wanka tare da suturta ta da farin likkafani a wurin da aka tsugunar da su.
Han Suofeiya, mahaifiyar yara uku, ta kasance daya daga cikin mutane sama da 130 da suka mutu sakamakon iftila'in girgizar kasa da ya auku da tsakar dare a yankin arewa maso yammacin China a makon nan, an binne ta da ɓaraguzan ginin gidan mahaifiyarta.
A yanayi na sanyin hunturu, mutanen da suka tsira a garin tantuna masu shudin launi, ba kawai suna cikin kuncin rasa matsugunansu da duk wani abu na more rayuwa ba ne kawai har da bakin ciki babba na asara ta mutuwar farat daya na 'yan uwansu.
Han Suofeiya ta kasance Musulma, kamar sauran mutanen da ke zaune a wannan yanki mai cike da tsaunuka da ke kusa da dadaddiyar hanyar da ake bi wajen kasuwanci da fitar da kayayyaki da kuma musayar ra'ayoyi da addinai tsakanin China da yankin Gabas ta Tsakiya da kuma Turai.
An binne ta ne a kauyen Yangwa da ke lardin Gansu kamar yadda ga al'adar al'ummar yankin ta tanada.
Maza da mata a cikin al'ummar sun yi ta kuka a bainar jama'a yayin da aka fito da gawarta daga matsugunin da aka ware wa danginta na wucin gadi inda aka ɗora ta a kan makara.
An ɗora wani ƙaton koren bargo da aka yi wa rubutu da harufan Larabci akan makarar da kusan mutum takwas suka dauka zuwa makabarta, sannan an yanka rago yayin da zaman makokin.
An yi jana'izar mutane uku da suka hada da karamin yaro a ranar Laraba, maza ne kawai suka halarci ainihin jana'izar.
Bayan sun yi addu’o’i ga duk mamatan, sai aka sanya gawarwakin da aka yi wa sutura da farin gyalle a ramukan da aka tona masu zurfi guda biyu da ke daf da juna a kasa.
Kanan Ma Yuanke mai shekaru 10 ne ya yi kokarin ciro shi daga baraguzan gidansu. (Han Suofeiya ta tafi ta zauna a gidan mahaifiyarta, sakamakon rashin lafiya da take fama da shi.)
Wani ɗan'uwan Ma ne ya rungume shi sosai yayin da suke kokawa a lokacin jana'izar, inda ya durkusa a kasa mai tsananin sanyi, yayin da ake binne mahaifiyarsa a cikin kabari.