Asibitoci sun yi gargadin cewa mutane da dama za su rasu saboda rashin kayan aiki.

A lokacin da Asibitin Indonesia na Gaza yake samu karuwar majinyata da suka samu munanan raunuka a dalilin hare-haren bama-baman Isra’ila, likitoci sun koma shirya wani dan wajen yin tiyata a barandar asibitin saboda asalin dakunan tiyatar sun cika, in ji su.

Saboda yadda karancin magunguna da rashin wutar lantarki da hare-haren bama-bamai suke shafar asibitoci, dole likitoci a Gaza suka koma aiki ba dare ba rana domin kula da majinyatan da ake kawo musu kusan a kowane lokaci.

“Muna yin awa daya-daya ne saboda ana iya kawo mana wadanda suka samu rauni a kowane lokaci.

"A lokuta da dama mukan yi tiyata a baranda, ko kuma a dakunan zaman masu kula da majinyata,” in ji Dokta Mohammed al Run.

Ya yi wannan jawabin ne jim kadan bayan harin bam ya bugi wani sashe a Asibitin Indonesia, wanda yake kusa da hanyar da sojojin Isra’ila ke kara ƙaimin kutsawa domin shiga yankin na Falasdinu mai dimbin mutane, da kuma yadda suke ganin alamar man fetur dinsu ya kusa karewa kamar yadda likitocin suka bayyana.

Tankokin Isra’ila sun shiga Gaza, mazaunin mutum miliyan 2.3 bayan kimanin mako uku suna jefa bama-bamai a yankin saboda mayar da martani a kan harin mayakan Hamas na ranar 7 ga Oktoba inda suka yi awon gaba da mutum 240 ’yan Isra’ila.

Ma’aikatan lafiya a yankin wanda ke karkashin Hamas sun ce an kashe sama da mutum 8,500 a hare-haren na Isra’ila a Gaza, ciki har da kananan yara 3,500.

A Arewacin Gaza, inda Isra’ila ta umarci miliyoyin mutane su bar gidajensu su koma Kudancin yankin, samun kiwon lafiya na cikin abubuwa da suka fi wahalar gaske.

Hari a Aibitin Kawancen Turkiyya

Ma’aikata a Asibitin Kawancen Turkiyya sun ce harin bam ya bugi dakin asibitin da ake kula da masu ciwon kansa.

“Harin ya matukar taba asibitin inda ya jawo injina da dama da suke aiki da wutar lantarki suka tsaya.

"Haka kuma hare-haren na baraza ga rayukan marasa lafiya da ma’aikatan kiwon lafiya,” in ji Dokta Sobi Skaik, daraktan asibitin, wanda shi kadai ne asibitin kula da ciwon kansa a yankin.

Duk da cewa an samu sauki bayan dawowar hanyar sadarwa a ranar Litinin bayan ta dauke baki daya a karshen makon jiya, mutanen Gaza suna fargabar sake katserwar hanyar ganawa da ’yan'uwansu nan gaba.

Ma’aikatan lafiya a yankin wanda ke karkashin Hamas sun ce an kashe sama da mutum 8,500 a hare-haren na Isra’ila a Gaza.

Idan ana aikin ceton rai na gaggawa da ma duk wani aikin kiwon lafiya, rashin hanyar sadarwa da intanet cikas ne babba.

A ranar Asabar, Elon Musk ya ce manhajar Starlink na Kamfanin X zai taimaka wajen samar da hanyar sadarwa tsakanin Gaza da ‘Amintattun kungiyoyin jinƙai na duniya.”

Sai dai Ministan Sadarwa na Isra’ila, Shlomo Karhi ya ce Isra’ila, “Za ta yi duk mai yiwuwa wajen hana yiwuwar hakan.”

Amma wasu daga cikin mazauna Gaza sun roki Musk da ya taimaka wajen samar musu da hanyar sadarwar.

“Muna Karni na 21 ne inda kusan komai ya dogara da intanet da sauran hanyoyin sadarwa da kuma wutar lantarki.

"Idan dukkan wadannan abubuwan suka katse, za a ware Gaza daga sauran duniya,” in ji Sobhi Abu Zaid, wanda yake gudun hijira a Asibitin Nasser a Khan Younis a Kudancin Gaza.

Katsewar wutar lantarki

Isra’ila ta mamaye Gaza, ta yanke wutar lantarki, sannan ta hana a shigar da man fetur, inda ta ce Hamas za ta iya amfani da fetur din domin hada kayan yaki.

Asibitoci sun yi gargadin cewa mutane da dama za su rasu a sanadiyar hakan domin ana bukatar janareta domin gudanar da wasu ayyukan ceton rayukan majinyata.

“Nan da wasu san’o’i, za a rasa wutar lantarki saboda rashin man fetur,” in ji likitan tiyata, Moaeen al Masry, sannan ya kara da cewa hakan zai kawo mutuwar majinyata da suke dakunan kula na musamman da dakunan tiyata.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Lafiyar Gaza, Ashraf al Qidra ya ce akwai yiwuwar za a kashe manyan janaretocin Asibitin Indonesia da na al Shifa da ke Gaza a ranar Laraba da daddare.

Isra’ila ta mamaye Gaza, ta yanke wutar lantarki, sannan ta hana a shigar da man fetur, inda ta ce Hamas za ta iya amfani da fetur din domin hada kayan yaki. 

Kakakin Rundunar sojin Isra’ila, Laftanar Kanar Jonathan Conricus ya ce Hamas na neman fetur ne domin hada kayan yaki.

“Akwai isasshen man fetur da za a yi amfani da shi na kwanaki a asibitoci, sannan akwai ruwan sha,” in ji shi.

A makon jiya, Asibitin Indonesia ya rasa fetur baki daya, wanda dole aka kashe wuta a mafi yawan dakunan asibitin.

Bayan sun samu karin man fetur, sai suka cigaba da aiki sosai, amma yanzu haka ya kusa karewa, inda za a koma gidan jiya, har zai iya tsayar da harkokin asibitin baki daya, in ji Masry.

Asibitin Indonesia akwai akalla majinyata guda 250 a yanzu, in ji Masry. Saboda asibitin yana kusa da inda ake gwabza yakin a Arewacin Gaza. Asibitin yana samun majinyata da dama da harin Isra’ila ya rutsa da su, in ji shi.

Tun lokacin da Isra’ila ta fara fadada hare-harenta a Gaza a ranar Juma’a, yankin Arewa na Beit Lahiya da Beit Hanoun suka kasance cikin matsanancin hare-hare.

Wani faifan bidiyo ya nuna yadda Falasdinawa suke daukar wadanda aka raunata a amalanke a ranar Talata daga Beit Hanoun.

TRT World