Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya yi kora ga kasashen Yammacin Duniya su zare kansu daga "laifukan yaki" da Isra'ila take aikatawa.
“Ya kamata kasashen Yammacin Duniya su nesanta kansu daga laifukan yakin da Isra'ila take yi. Duk wani nuna goyon baya ga Isra'ila na nufin an amince ta ci gaba da kashe karin Falasdinawa,” kamar yadda Fidan ya bayyana ranar Juma'a a wurin taro kan Tsare-Tsare kan harkokin sadarwa na kasashen duniya (Stratcom) a birnin Istanbul.
"Tarihi ba zai manta da rashin kaunar da ake nuna wa turar Falasdinawa ba Turai," inda aka amince da kona Alkur'ani a matsayin fadar albarkacin baki," in ji Minista Fidan.
Ya kara da cewa za a samu dauwamammen zaman lafiya ne kawai idan aka yi adalci da hadin kan kasashen duniya da gaskiya.
Watsa labaran karya a kan Gaza
Fidan ya ce irin labaran karyar da aka rika watsawa a Afghanistan da Iraki har ta kai ga an afka mus da yaki, yanzu ma ana watsa su a kan Gaza.
Ya ce akwai labaran karya iri biyu da ake watsawa game da “laifukan yakin da Isra'ila take aikatawa a Gaza da Gabar Yammacin Kogin Jordan” bayan harin ba-zata da Hamas ta kai mata ranar 7 ga watan Oktoba.
“Na farko shi ne nuna son kai na kafafen watsa labaran Yammacin Duniya wadanda suka kawar da kai game da ukubar da aka jefa Falasdinawa a ciki. Sai kuma watsa labaran karya da gangan, wanda bai tsaya kan abubuwan da suka faru ranar 7 ga watan Oktoba ba, inda Isra'ila take kokarin boye wa duniya ta'asar da take yi.”
Laifukan yaki da Isra'ila take aikatawa a yankin Gaza
Fidan ya ce bai kamata wani ya halasta “rashin imani na kashe-kashen da Isra'ila take yi wa al'ummar Gaza ba” da sunan kare kanta.
“Bai kamata mu bari Isra'ila ta rufe laifin yaki daya bayan daya ba. Don haka, dole mu samu mafita ta dindindin ta hanyar sabuwar tattaunawa da tsare-tsare,” in ji shi.
Fidan ya ce babban burin Tel Aviv shi ne kada a tabbatar da tsarin kasancewar kasashe biyu masu 'yancin kansu, inda take daukar matakai a Birnin Kudus da Gabar Yammacin Kogin Jordan da Gaza.
Ya kara da cewa: “Kowa ya yarda cewa mafiya daya ita ce a samar da kasashe biyu na Isra'ila da Falasdinawa masu cin gashin kansu, inda Gabashin Birnin Kudus zai kasance babban birnin Falasdinu.”
Fidan ya jaddada cewa Turkiyya ba za ta taba gazawa wurin yin abin da ya dace ba da kuma goyon bayan fafutukar Falasdinawa.