1441 GMT –– Jami'an Amurka da Isra'ila da UAE sun tattauna shirin bayan yaƙin Gaza
Jami'ai daga kasashen Amurka da Isra'ila da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gudanar da wani taro domin tattauna shirin Gaza bayan kawo ƙarshen yaƙin, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.
Kamfanin dillancin labaran Axios ya ambato wasu majiyoyin Isra'ila biyu cewa an gudanar da taron ne a Abu Dhabi.
Taron, wanda Ministan Harkokin Wajen Hadaddiyar Daular Larabawa Abdullah bin Zayed Al Nahyan ya karbi bakunci ya samu halartar mashawarcin Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka Brett McGurk da Ministan Harkokin Dabarun Isra'ila Ron Dermer.
Wasu manyan jami'an tsaron Isra'ila biyu da ke aiki kan shawarwarin Isra'ila na shirin da ake da shi ga Gaza sun raka Dermer zuwa Abu Dhabin, in ji jami'an.
1017 GMT –– Yawan Falasɗinawan da suka mutu a Gaza saboda yaƙin Isra'ila sun kai 39,090
Sojojin Isra'ila sun kashe wasu Falasdinawa 84 a hare-haren da suka kai a Gaza, wanda ya kai adadin wadanda suka mutu ya kai 39,090 tun daga ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata, in ji Ma'aikatar Lafiya a yankin.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ƙara da cewa wasu 90,147 sun jikkata a harin.
"Sojojin Isra'ila sun kashe mutum 84 tare da raunata wasu 329 a 'kisan kiyashi' guda takwas da aka yi wa iyalai a cikin sa'o'i 24 da suka gabata," in ji ma'aikatar, tare da bayyana cewa an kashe 73 daga cikinsu a Khan Younis da ke kudancin Gaza.
Ta ƙara da cewa "har yanzu mutane da dama na maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine da kuma kan tituna yayin da masu ceto suka kasa kai musu ɗauki."
0944 GMT –– WHO na ganin 'babbar barazana' ta yaɗuwar cutar shan inna a faɗin Gaza
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce, akwai babban hadarin kamuwa da cutar shan inna a Gaza da ma gaba da iyakokinta, saboda yanayin rashin lafiya da tsaftar muhalli a yankin Falasdinawa da ke fama da yaƙi.
Ayadil Saparbekov, jagoran tawagar gaggawa na kiwon lafiya a WHO a Gaza da kuma Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, ya ce an ware nau'in cutar shan inna ta 2 da aka samu daga samfuran muhalli daga najasa a Gaza.
"Akwai babban hadarin yada cutar shan inna da ke yaduwa a Zirin Gaza, ba wai kawai don gano cutar ba amma saboda tsananin yanayin da ake ciki na tsaftar ruwa," kamar yadda ya shaida wa manema labarai a Geneva ta hanyar bidiyo daga Kudus.
"Hakanan cutar tana iya yaɗuwa a duniya, a wani matsayi mai girma."
0431 GMT –– Ministan Harkokin Wajen China Wang Yi ya yaba game da matakin da ƙungiyoyin Falasɗinawa 14 suka amince da shi na kafa "gwamnatin riƙon-ƙwarya ta haɗin-kan ƙasa" da za ta jagoranci Gaza bayana yaƙi.
Ɓangagorin da suka haɗa da ƙungiyar Hamas da Fatah sun gana a Beijing a wannan makon a wani sabon yunƙuri na yin sulhu a tsakaninsu.
A yayin da ake kammala taron, Ministanr Harkokin Wajen China ya ce ɓangarorin sun amince su yi "sulhu".
"Babbar nasarar da aka samu ita ce amincewar da aka yi a kafa gwamnatin riƙon-ƙwarya ta haɗin-kan ƙasa domin gudanar da mulkin Gaza bayan kammala yaƙi," in ji Wang jim kaɗan bayan ɓangarorin sun sanya hannu a kan "Yarjejeniyar Beijing" a babban birnin China.
"Sulhu abu ne da ya kamata ɓangarorin Falasɗinawa su yi a cikin gida, amma kuma a lokaci ɗaya, ba za a iya cim masa ba, ba tare da goyon bayan ƙasashen duniya," a cewar Wang.
2100 GMT — Masu goyon bayan Falasɗinawa a Amurka sun yi zanga-zanga kan zuwan Netanyahu ƙasar
Masu goyon bayan Falasɗinawa a Amurka sun taru a wajen otal ɗin Watergate da ke Washington DC, inda Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sauka gabanin ya yi jawabi ga zauren majalisar dokokin ƙasar ranar Laraba.
Masu zanga-zangar suna riƙe da kwalaye da aka rubuta: "A kama Netanyahu" da kuma "Mai laifin yaƙi yana cikin wannan otal ɗin," sua nufin Firaminista Netanyahu wanda ke da alhakin kisan dubban Falasɗinaa fararen-hula a Gaza.
Kazalika ana shirin gudanar da wata gagarumar zanga-zangar ranar Laraba a yayin da Netanyahu zai gabatar da jawabi ga 'yan majalisar dokokin Amurka a yayin da ƙasarsa ke ci gaba da luguden wuta a Gaza.
2222 GMT — Biden ya sha alwashin 'ci gaba da aiki domin kawo ƙarshen yaƙin Gaza'
Shugaban Amurka Joe Biden ya sha alwashin ci gaba da aiki domin ganin an kawo ƙarshen yaƙin Gaza har zuwa ƙarshen wa'adinsa na mulki bayan ya fasa sake tsayawa takara.
"Zan ci gaba da aiki kafaɗa-dakafaɗa da Isra'ila da Falasɗinawa domin ƙoƙarin ganin yadda za a kawo ƙarshen yaƙin Gaza, da kuma tabbatar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, tare da tabbatar da ganin waɗanda aka yi garkuwa da su sun koma gida," in ji Biden a wani jawabi da ya yi a hedkwatar yaƙin neman zaɓensa, wadda ya mayar ta goyon bayan takarar shugabancin ƙasar mataimakiyarsa Kamala Harris.