Al'ummar Musulmai a Jamus na ci gaba da fuskantar damuwa da fargaba. /Hoto: AA

Yawan ire-iren wasikun barazana da ake aikewa masallatai a Jamus na daɗa ƙaruwa tun bayan fara yakin Gaza da Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

A cewar wata sanarwa da sashen da ke sa ido kan nuna wariya na kungiyar hadin kan harkokin Musulmai ta Turkiyya DITIB a yankin arewacin birnin Cologne ya fitar, an bayyana cewa, an aika da wasu wasiku da sakon 'Email' da dama da ke kunshe da cin zarafi da barazana ga masallatai a kasar Jamus.

Babban Masallacin Cologne kadai ya samu irin wadannan wasiku da sakonnin Email guda 17, sannan a baya-bayan nan an kai hari Masallacin DITIB Selimiye da ke yankin arewacin Dinslaken.

Al'ummar Musulmai suna cikin tashin hankali kan wannan batu, in ji sanarwar.

Kyamar Musulmai da 'yan gudun hijira

A watan da ya gabata ma wani masallaci a birnin Munster da ke yammacin Jamus ya samu wata wasikar barazana wadda ke ƙunshe da cin mutuncin da zarafin Musulmai da 'yan gudun hijira.

Kazalika wasiƙar na ƙunshe da kalaman nuna wariyar launin fata, ciki har da "Jamus sai Bajamushe, baƙi su yi waje."

Shugaban kungiyar manyan masallatai ta birnin Munster Fettah Cavus ya bayyana cewa, abin bakin cikin shi ne ayyukan nuna ƙyamar baki da Musulmai na ƙaruwa a Jamus.

TRT World