Jami'an hukumar leƙen asirin Amurka sun kawar da Donald Trump daga kan dandamalin da yake jawabi a wani wurin gangamin yaƙin neman zaɓe a jihar Pennsylvania bayan wani mutum ya harbe shi.
A yayin da ya ji ƙarar harbin, an ga Trump ya ɓata rai sannan ya rufe kunnensa na dama, wanda daga baya aka ga yana zubar da jini.
Jami'an hukumar leƙen asiri sun garzaya dandamalin, inda suka yi ƙawanya ga ɗan takarar shugaban na Amurka na jam'iyyar Republican sannan suka yi masa rakiya ya sauka daga kansa, a yayin da Trump ya ɗaga hannunsa ga dandazon mahalarta gangamin don nuna alamar rashin karaya.
Wannan lamari mai tayar da hankali ya ƙara dugunzuma ƙasar da tuni take cikin zaman ɗarɗar na rashin tabbas game da siyasarta gabanin fafatawar da za a yi a zaɓen shugaban ƙasa tsakanin Trump da Joe Biden a watan Nuwamba mai zuwa.
"Tsohon shugaban ƙasar yana cikin aminci," a cewar hukumar leƙen asirin Amurka a saƙon da ta wallafa a shafin X.
Ofishin yaƙin neman zaɓensa ya ce yana "cikin aminci" kuma ana duba lafiyarsa a wata cibiyar kula da lafiya.
"Shugaba Trump yana godiya ga hukumomin tsaro da kuma waɗanda sukasoma kai masa ɗauki yayin faruwar wannan mummunan lamari. Yana cikin aminci kuma ana duba lafiyarsa a wata cibiyar kula da lafiya. Za mu yi ƙarin bayani nan gaba," a cewar wata sanarwa da kakakin ofishin yaƙin neman zaɓensa Steven Cheung ya fitar.
Lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan Trump ya soma jawabi a wurin gangaminsa na ƙarshe na yaƙin neman zaɓe gabanin Babban Taron Ƙasa na Jam'iyyar Republican da za a yi a Milwaukee a makon gobe.
Gangamin, wanda aka gudanar a garin Butler na jihar Pennsylvania, ya kaure da yamutsi da iface-iface bayan an ji harbin bindiga.
An ji Trump yana cewa, "bari na sanya takalmana" a yayin da jami'an hukumar leken asiri suke taimaka masa don ya tashi tsaye.
Daga bisani jami'an leken asiri sun ɗauki Trump mai shekara 78 suka shigar da shi mota ƙirar SUV, a yayin da ya ɗaga hannunsa yana jinjina da ke nuna alamar bai karaya ba.