Ana zaton jirgin ya fadi ne a wani tsauni da ke arewa maso gabashin Afghanistan. / Hoto: Reuters / Photo: Reuters Archive

Wani jirgin fasinja ya fadi a arewa maso gabashin Afghanistan a kan tsaunuka, kamar yadda jami'an lardin da lamarin ya faru suka tabbatar.

Jirgin saman ya yi hatsari ne a lardin Badakhsan a ranar Lahadi, wanda ke da iyaka da China da Tajikistan da Pakistan, sai dai babu tabbaci kan daidai wurin da jirgin ya yi hatsari.

Zabihullah Amiri, wanda jami'in watsa labarai da al'adu ne na lardin ya bayyana cewa tuni aka aika da jami'ai wurin da hatsarin ya faru a yankin Topkhana wanda ke a gundumar Kuran-wa-Munjan.

"Jirgin saman ya yi hatsari amma ba a san takamaimai wurin da ya fadi ba. Mun tura jami'ai sai dai ba su dawo ba," kamar yadda Amiri ya bayyana ba tare da wani karin bayani ba.

"Jama'ar gari ne suka gaya mana hakan da safe," in ji shi.

Tsaunin Hindu Kush ya bi ta lardin wanda a nan tsauni mafi tsawo a Afghanistan yake, wato tsaunin Noshaq inda yake da tsawon mita 7,492.

Hukumar da ke sa ido kan zirga-zirgar jiragen sama ta Rasha Rosaviatsia ta bayyana cewa wani karamin jirgin fasinja da ke hanyar zuwa Moscow daga Indiya ya batan-dabo a Afghanistan.

Hukumar ta ce jirgin kirar Falcon 10 jet, yana da rajista a Rasha kuma akai mutum shida a cikinsa, daga ciki akwai ma'aikatan jirgin hudu da fasinja biyu.

Reuters