Mai ƙin jinin Addinin Islama Tommy Robinson wanda aka taɓa kamawa da laifi. / Hoto: AA

Kisan da aka yi wa wasu mata matasa uku a wani gidan rawa a Birtaniya a farkon makon jiya ya tayar da tarzoma, lamarin da ya jawo arangama tsakanin gungun masu tsananin ra'ayin riƙau da masu adawa da wariyar launin fata.

Kusan mutum 400 aka kama tun bayan soma tarzomar, wadda ta laƙume wuraren kasuwanci da dama da kuma lalata wuraren al'umma.

A lokacin da editar kafar watsa labarai ta Al Jazeera ta Turai Anealla Safdar ta fuskanci cin zarafi a kan titi a wani birni mai zaman lafiya na Tonbridge, waɗanda suka aikata hakan sun yi ta kiran sunan "Tommy, Tommy, Tommy Robinson".

Wannan sunan wanda wasu "gungun fararen-fata 'yan shekara 16" suka rinƙa faɗa wa Safdar, ya firgita ta tare da 'ya'yanta mata biyu waɗanda ke da shekara huɗu zuwa shida a yayin da suke tafiya a kan titi a mahaifarsu.

"Wannan ba daidai ba ne," kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.

Wane ne Tommy Robinson, sunan da ya zauna a bakunan masu gangamin nuna fifikon farar-fata a faɗin Birtaniya?

An haife shi a matsayin Stephen Christopher Yaxley-Lennon a 1982 a Ingila, Robinson wanda Baturen Ingila ne da ke kamfe na ƙin jinin Musulunci yana daga cikin fitattun masu tsattsauran ra'ayi a Birtaniya. Haka kuma kotu ta taɓa samunsa da laifi.

Duk da cewa mai shekara 17 ɗan Birtaniya, Axel Muganwa Rudakubana daga Lancashire ana zarginsa da kai wannan harin, masu fifita farar-fata na ci gaba da kai hari ga marasa rinjaye, inda suke cewa ana ikirari a shafukan sada zumunta kan cewa wani mai neman mafaka ne Musulmi wanda ya shiga Birtaniya a 2023 a cikin wani ƙaramin kwale-kwale ya kai harin.

Ga wasu daga cikin muhimman bayanai game da Robinson, mutumin da ake zargi da tada zaune tsaye da kuma jagorantar tarzomar masu tsattsauran ra'ayin a wajen Birtaniya.

- Yadda Robinson ya girma a Luton, wani gari da ke da masu launin fata da addinai daban-daban, hakan ya taka rawa sosai wurin cusa masa irin wannan ra'ayin nasa.

Mahaifiyarsa 'yar ci rani ce daga Ireland. Ya halarci makarantar Putteridge inda ya ce ya sha ganin faɗan "'yan daba" wanda wariyar launin fata ya jawo.

-Tarihinsa wanda aka rubuta mai suna, Maƙiyin Ƙasa, na ɗauke da jerin bayanai dangane da faɗace-faɗacen da ake zargin ya yi na daba.

Har ila yau ya bayyana koke-koke na ƙashin kansa da suka haɗa da rashin gayyatar daurin auren wasu abokansa Musulmai guda biyu, Kamram da Imram, wadanda ya kulla alaka da su a makaranta bayan sun tara kudin sayen Porsche tare.

-Ya samo sunan "Tommy Robinson" a 2009, inda ya samo sunan daga wani ɗan ƙwallo wanda ɗan daba ne kuma ɗan asalin garin Luton, domin ware abubuwan da yake yi na tsattsauran ra'ayi da rayuwarsa.

- A shekarar 2009, Robinson an haɗa kai da shi domin ƙirƙiro ƙungiyar English Defence League wato EDL, wadda ƙungiya ce mai tsattsauran ra'ayin ƙin jinin Musulunci, inda suke ikirarin martani ne ga Muslumai masu tsattsauran ra'ayi a Birtaniya.

- A ƙarƙashin mulkin Robinson, EDL ta shirya zanga-zanga irin daban-daban wadda yawanci aka rinƙa samun arangama da 'yan sanda da masu adawa da su. An rinƙa Allah wadai da irin wannan zanga-zangar wadda ke ƙara goyon bayan ƙin jinin Musulmai.

A shekarar 2011, an kama shi da laifin jagorantar wani rikici a kan titi wanda ya haɗa da kimanin mutum 100 tare da aika shi gidan yari na tsawon watanni 12.

- A cikin 2014, an yanke wa Robinson hukuncin ɗaurin watanni 18 a gidan yari saboda zamba, zargin da ba shi da alaka da harkokin siyasa. Ya yarda cewa ya yi amfani da bayanan karya don samun jinginar gida fiye da dala 200,000 a halin yanzu.

-Robinson ya bar EDL a watan Oktoban 2013, yana mai bayyana cewa baya son jagorantar wani yunkuri da ya yi imanin cewa masu tsattsauran ra'ayi da masu wariyar launin fata na neman ƙwace iko da ƙungiyar.

Bayan ya bar EDL, sai Robinson ya soma aiki da Quilliam, wanda cibiyar yaƙi da tsattsauran ra'ayi inda daga baya ya zama wakilin wata kafar watsa labarai ta masu tsattsauran ra'ayi ta Canada mai suna Rebel Media.

-Robinson ya ci gaba da mayar da hankali bayan tarayyarsa da EDL inda ya ci gaba da zanga-zanga kan Musulmai a Birtaniya.

-A Mayun 2018, an kama Robinson sakamakon ɗaukar bidiyo kai tsaye a wajen kotu lokacin da ake wata shari'a, wadda tuni kuma aka haramta yin rahoto kai tsaye kan shari'ar. An kama shi da laifin raina umarnin kotu tare da aika shi gidan yari na tsawon watanni 13.

- Ɗaurin da aka yi masa ya jawo zanga-zanga daga magoya bayansa musamman waɗanda ke a Birtaniya da Amurka, waɗanda ke kallonsa a matsayin "shahidi ta ɓangaren tofa albarkacin baki".

Sai dai wasu da dama sun caccaki abubuwan da ya yi tare da kiran ƙungiyar da yake jagoranta ta masu tsattsauran ra'ayi da wadda ke so ta yi karan-tsaye kan dimokuraɗiyya.

- An soke hukuncin farko na Robinson a kotun daukaka kara, kuma an sake shi daga gidan yari a watan Agustan 2018. Duk da haka, an sake gurfanar da shi a gaban kotu, wanda ya sa aka yanke masa hukuncin watanni tara.

- A shekarar 2019, Robinson ya tsaya takara a matsayin dan takara mai cin gashin kansa a zaben Majalisar Dokokin Turai, mai wakiltar mazabar North West England. Ya kasa samun kujera, inda ya samu kashi 2.2 cikin 100 na kuri'un da aka kaɗa.

- Robinson ya rubuta littafai da dama kuma ya fito a cikin fina-finan da suka shafi Musulunci da shige da fice a Birtaniya. Ana sukar waɗannan ayyuka sau da yawa don yada rashin fahimta da kuma haifar da rarrabuwa.

- Robinson ya fuskanci matsalolin kudi, ciki har da an umarce shi da ya biya fiye da dala 127,000 a matsayin diyya a shekarar 2021 bayan ya sha kaye a wata shari'ar ɓatanci da wani dan gudun hijirar Syria ya kai shi ƙara inda ya zarge shi da laifin tashin hankali.

- An dakatar da shi daga Facebook da Instagram saboda saɓa manufofinsu kan kalaman ƙiyayya da haɓaka tsattsauran ra'ayi. An kuma dakatar da shi daga Twitter (yanzu X), amma an mayar da shafin nasa bayan da Elon Musk ya sayi dandalin sada zumuntar.

- Duk da waɗannan koma bayan, Robinson ya ci gaba da kasancewa mai ƙwazo yayin da yake fitar da bidiyo a intanet.

TRT World