Ana kallon Ismail Haniyeh a matsayin mai sassaucin ra'ayi idan an kwatanta shi da sauran mambobin Hamas masu tsattsauran ra'ayi. / Hoto: Reuters

Ismail Haniyeh, jagoran Hamas da Isra'ila ta yi wa kisan gilla a Iran, wani jajirtaccen mai faɗa a ji ne da ke ɓangaren diflomasiyya na ƙungiyar Hamas ta Falasɗinu. A baya, yayin da yaƙi ke ci gaba da ƙamari a Gaza, wani harin Isra'ila ya kashe uku cikin 'ya'yansa maza.

Amma yawa-yawan jami'an diflomasiyya suna kallonsa a matsayin mai sassaucin ra'ayi idan aka kwatanta shi da sauran mambobin Hamas masu tsattsauran ra'ayi a Gaza.

An naɗa Haniyeh kan babban muƙami na jagorancin Hamas a 2017, kuma yakan yi ziyara tsakanin Türkiye da babban birnin Qatar, Doha, inda yake zille wa shingayen tafiye-tafiye a Gaza. Wannan ya ba shi damar aiki a matsayin mai sasantawa don tsagaita wuta ko magana da Iran.

"Duka yarjeniyoyi na sasantawa da ku (ƙasashen Larabawa) kuka yi da (Isra'ila) ba za su kawo ƙarshen wannan rikici ba," Haniyeh ya faɗa a tashar talabijin ta Al Jazeera ta Qatar jim kaɗan bayan mayaƙan Hamas sun ƙaddamar da harin 7 ga Oktoba.

Martanin Isra'ila kan harin na Hamas ya kashe sama da mutane 39,000 cikin Gaza zuwa yanzu, a cewar hukumomin lafiya na yankin, yayin da a faɗin duniya ake ta zanga-zangar ƙyamar yaƙin ƙare-dangi da Isra'ila ke yi kan Falasɗinawa.

Yadda Haniyeh ya shiga siyasa

Sanda yake matashi, Ismail Haniyeh ɗalibi ne ɗan gwagwarmaya a Jami'ar Islamic University a birnin Gaza. Ya shiga Hamas lokacin da aka ƙirƙire ta yayin boren Intifada na Farko a 1987.

An kama shi kuma aka fitar da shi daga yankin na ɗan lokaci.

Haniyeh ya gina alaƙar kusanci da wanda ya kafa Hamas, Sheikh Ahmad Yassin, wanda shi ma ɗan gudun hijira ne daga ƙauyen Al Jura kusa da Ashkelon, kamar yadda dangin Haniyeh suke.

A 1994, ya faɗa wa Reuters cewa Yassin abin koyi ne ga matasan Falasɗinawa, inda ya ambata cewa: "Muna koyi da soyayyarsa ga Musulunci da sadaukarwa ga Musulunci, da ƙin durƙusawa waɗannan azzaluman da masu kama-karya."

Zuwa 2003 Haniyeh ya zama amintaccen hadimin Yassin, inda aka taɓa ganin hotonsa a gidan Yassin na Gaza yana riƙe waya a kunnen shugaban Hamas, wanda kusan gaba ɗayan jikinsa ya shanye.

Isra'ila ta halaka Sheik Yassin a 2004.

Haniyeh ya kasance kan gaba wajen ra'ayin Hamas ta shiga siyasa. A 1994, ya ce kafa jam'iyyar siyasa "zai taimaka wa Hamas ta shirya wa lamuran da ke faruwa".

Da fari, shugabannin Hamas sun ƙi karɓar wannan ra'ayi, amma daga baya sun amince, inda Haniyeh ya zama Firaministan Falasɗinu bayan da ƙungiyar ta lashe zaɓen majalisar Falasɗinu na 2006, shekara ɗaya bayan sojin Isra'ila sun janye daga Gaza.

Ƙungiyar Hamas ta karɓe iko da Gaza a 2007.

A 2012, da 'yan rahoto suka tambaye shi ko Hamas ta yi watsi da amfani da makami don yaƙar mamayar Isra'ila kan yankunan Falasɗinu, Haniyeh ya amsa cewa, "Tabbas ba haka ba ne" sannan ya ce tirjiyar za ta ci gaba "cikin duka salo - tirjiyar jama'a, siyasa, diflomasiyya da soji".

'Fuskar siyasa da diflomasiyya ta Hamas'

Lokacin da Haniyeh ya bar Gaza a 2017, wanda ya gaje shi shi ne Yahya Sinwar, wani mai ra'ayin riƙau da ya kwashe sama da shekaru 20 a gidan yarin Isra'ila, kuma wanda Haniyeh ya yi maraba da dawowarsa Gaza a 2011 bayan musayar fursunoni.

"Haniyeh na jagorantar yaƙi a fagen siyasa domin Hamas, tare da gwamnatocin ƙasashen Larabawa," cewar Adeeb Ziadeh, wani ƙwararre kan harkokin Falasɗinu a Jami'ar Qatar University. Ziadeh ya faɗa kafin rasuwar Haniyeh, cewa Haniyeh yana da kusanci da manyan dakarun ɓangaren soji na ƙungiyar.

"Shi ne fuskar siyasa da diflomasiyya na Hamas," in ji Ziadeh.

Haniyeh da Meshaal sun gana da jami'ai a Masar, wadda ita ma ta shiga tsakani a tattaunawar tsagaita wuta. Gidan watsa labarai na gwamnatin Iran ya ruwaito cewa Haniyeh ya je Tehran a farkon Nuwamba don ganawa da Shugaban Addini na Iran, Ali Khamenei.

Manyan jami'ai guda uku sun gaya wa Reuters cewa Khamenei ya faɗa wa jagoran Hamas a ganawar cewa Iran ba za ta shiga yaƙin ba, kasancewar ba a sanar da ita ba gabanin fara shi.

Harin Isra'ila ya hallaka 'ya'ya da jikokin Haniyeh

Ismail Haniyeh ya rasa mutane 60 daga danginsa — har da 'ya'ya maza uku tun bayan da Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙin ƙare-dangi kan Gaza, ranar 7 ga Oktoba.

Uku cikin 'ya'yan Haniyeh maza - Hazem, Amir da Mohammad - an kashe su ranar 10 ga Afrilu lokacin da harin jirgin yaƙin Isra'ila ya sami motar da suke ciki, cewar Hamas.

Haka nan Haniyeh ya rasa huɗu cikin jikokinsa, yara uku mata da ɗaya namiji, a wannan harin.

Haniyeh ya musanta iƙirarin Isra'ila cewa 'ya'yansa mayaƙa ne na ƙungiyar, kuma ya ce, "Manufofin al'ummar Falasɗinu suna gaba da komai", lokacin da aka tambaye shi ko kashe iyalansa zai shafi tattaunawar tsagaita wuta.

Haniyeh ya ce, "Idan azzaluman abokan gaba suna tunanin kai hari kan iyalaina zai sa mu sauya matsayarmu ko tirjiyarmu, to su sani cewa suna yaudarar kansu saboda duka shahidi a Gaza da Falasɗinu iyalaina ne".

"Jinin shahidanmu shaida ce ta cewa ka da mu ba da kai, kuma ka da mu sauya, ka da mu karaya, amma dai mu ci gaba da bin tafarkinmu da jajircewa."

TRT World