Wakiliyar MDD ta buƙaci a ƙaƙaba wa Isra'ila takunkuman samun makamai kan kisan kare dangin da take yi a Gaza / Photo: AFP

1359 GMT — Wakiliyar MDD ta buƙaci a ƙaƙaba wa Isra'ila takunkuman samun makamai kan kisan kare dangin da take yi a Gaza

Wata ƙwararriya ta Majalisar Dinkin Duniya ta shaida wa hukumar kare hakkin bil adama ta duniya cewa ta yi imanin cewa yakin da Isra'ila ta yi a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai na kisan ƙare dangi, ta kuma yi kira ga kasashen da su gaggauta ƙaƙaba takunkumi ciki har da na hana ta samun makamai.

"Na gano cewa akwai dalilai masu ma'ana da za a yarda da cewa ana yi wa Falasɗinwa kisan ƙare dangi a Gaza," a cewar Francesca Albanese, mai kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta musamman a yankunan da aka mamaye, kamar yadda ta shaida wa hukumar kare hakkin bil adama ta MDD a Geneva.

1236 GMT — Tankokin yaƙin Isra'ila sun yi wa asibitin Nasser da ke Gaza ƙawanya

Gomman tankokin yaƙin Isra’ila da motoci masu sulke sun yi wa asibitin Nasser da ke Gaza ƙawanya, wanda wuri ne da dubban Falasɗinawa ke neman mafaka, kamar yadda shaidu suka tabbatar.

Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an buɗe wuta kan ginin asibitin da ke kudancin Khan Younis, amma sojojin ba su kutsa ciki ba.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana cewa sojojin Isra’ila sun ta harbi tare da kai samame a kewayen asibitin domin shirya kutsawa cikin asibitin.

Ma’aikatar ta kuma tabbatar da cewa akwai dubban mutanen da suka rasa muhallansu waɗanda suka samu mafaka a asibitin kuma suna fama da ƙarancin ruwa da abinci.

0832 GMT — Shugaban Hamas Ismail Haniyeh ya kai ziyara Iran

Shugaban Hamas Ismail Haniyeh ya isa Tehran a ranar Talata domin tattaunawa da jami’an Iran kwana guda bayan da Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi kira ga tsagaita wuta a yaƙin da Isra’ila ke yi da Gaza.

“Shugaban Hamas Ismail Haniyeh a lokacin ziyararsa a Tehran a ranar Talata zai haɗu da Ministan Harkokin Wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian,” kamar yadda kafar watsa labarai ta IRNA ta ruwaito.

Wannan ce ziyara ta biyu da shugaban na Hamas ya kai Tehran tun bayan da Hamas ɗin ta ƙaddamar da hari a Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

2154 GMT — Hamas ta shirya wa tsagaita wuta na dindindin a Gaza

Ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa ta Hamas ta ce ta sanar da masu shiga tsakani cewa za ta ci gaba da bin shawarwarinta na farko na cim ma matsayar tsagaita wuta da ta haɗa da janye sojojin Isra'ila daga Gaza da kuma mayar da Falasɗinawan da suka yi gudun hijira zuwa yankunansu.

Har ila yau, ta buƙaci abin da ta kira "musayar fursunoni na gaske", dangane da sakin fursunonin Falasɗinawa daga gidajen yarin Isra'ila domin musanya da Isra'ilawan da take garkuwa a Gaza.

Hamas ta gabatar da shawarar tsagaita wuta a Gaza ga masu shiga tsakani da Amurka a tsakiyar watan Maris da ta haɗa da sakin fursunonin Isra'ila da aka yi garkuwa da su domin samun ƴanci ga fursunonin Falasdinu, waɗanda 100 daga cikinsu ke zaman ɗaurin rai-da-rai, kamar yadda shawarar da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani ta bayyana.

Masar da Qatar dai na ƙoƙarin takaita bambance-bambancen da ke tsakanin Isra'ila da Hamas game da yadda yarjejeniyar tsagaita wuta ta kasance, sakamakon yadda matsalar jinƙai ke ƙara ƙamari da al'ummar Gaza ke fuskantar barazanar yunwa.

Hamas ta ce farkon sakin ƴan Isra’ilan zai hada da mata da ƙananan yara da tsofaffi da marasa lafiya a matsayin wadanda aka yi garkuwa da su domin sakin Falasɗinawa 700-1000 da ake tsare da su a gidajen yarin Isra’ila, a cewar shawarar. An sanya batun sakin ''mata ƙanana sojoji'' na Isra'ila a ciki.

2316 GMT — Netanyahu ya ji takaicin yadda Amurka ta ƙaurace wa ƙudurin tsagaita wuta na Majalisar Dinkin Duniya: Sanata

Ran Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ɓaci bayan amincewa da ƙudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan tsagaita wuta a Gaza, in ji Sanata Bernie Sanders.

"Ran Netanyahu ya ɓaci. Ya soke wata zuwan wata tawaga birnin DC saboda Amurka ta ƙaurace wa ƙudurin da ke neman tsagaita wuta," in ji Sanders a X.

Ya ƙara da cewa "Amma takaicin da ya jin bai kai yadda zai ƙi karɓar dalar Amurka biliyan 3.3 na masu biyan haraji ba da nufin tallafa wa yaƙinsa na rashin ɗa'a. Ba za a sake bai Netanyahu kuɗaɗen da zai kashe yaran Falasdinawa da yunwa ba."

TRT Afrika da abokan hulda