Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a kullum a Gaza wadanda akasarinsu mata ne da yara. / Hoto: AA

1100 GMT — Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan Falasɗinu ta zargi Isra’ila da aikata kisan kiyashi a Gaza.

A yayin da take alaƙanta Gaza da “sansanin gudun hijira mafi girma da kuma kunya a ƙarni na 21,” Francesca Albanese ta wallafa a shafinta na X cewa Isra’ila na aikata kisan kiyashi a kan unguwanni da asibitoci da makarantu da sansanonin gudun hijira da mafaka duk a lokaci guda.

Zargin na Albanese na zuwa ne bayan wani hari da aka kai a ranar Asabar inda Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 100 ta kuma jikkata da dama a wani hari da ta kai wata makaranta a Birnin Gaza.

0230 GMT — Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 100 ta kuma jikkata da dama a wani hari da ta kai wata makaranta a Birnin Gaza, kamar yadda kamfanin dillancin labaran gwamnati na WAFA ya bayyana.

Kamfanin dillancin labaran na Falasɗinawa WAFA ya ce tankokin yaƙin Isra'ila sun yi luguden wuta kan makarantar, wacce ta zama mafaka ga Falasɗinawan da suka rasa gidajensu.

"An yi wa fiye da mutum 40 shahada an jikkata da dama bayan harin na Isra'ila a makarantar Al-Tabai'een a yankin Al-Sahaba a Birnin Gaza," kamar yadda mai magana da yawun 'yan sandan yankin Mahmoud Basal ya wallafa tun da farko a saƙon da ya wallafa a Telegram.

0052 GMT — An kai wa sojojin Amurka hari a Syria

An kai wa sojojin Amurka hari da jirage marasa matuƙa a Syria, kamar yadda wani jami'in ƙasar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, duk da dai babu wanda ya ji rauni kamar yadda rahotannin farko-farko suka nuna.

"Rahotannin farko ba su nuna cewa an samu wanda ya ji rauni ba, sai dai jami'an lafiya na ci gaba da duba abubuwan da suka faru a wajen. A yanzu haka muna nazari kan ɓarnar da aka yi," kamar yadda jami'in wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana.

Amurka tana da sojoji da dama a Gabas ta Tsakiya, da adadinsu ya kai kimanin 45,000, da sansanoni da dama, da jiragen yaƙi na sama da na ruwa da yawa, abin da ya sa ake nuna damuwa kan yiwuwar ɓarkewar yaƙi a yankin.

A yanzu haka Amurka na da dakaru na musamman da sojoji kimanin 900 a Syria don taimaka wa ƙungiyar ta'addanci ta YPG/PKK, wacce take amfani da sunan SDF.

Amurka na da na ƙananan sansanoni kamar wajen haƙar mai na al-Omar da Al-Shaddadi, mafi yawa a arewa maso gabashin ƙasar, da kuma wani ƙaramin sansanin tsaro na soji, da aka fi sani da sansanin Al-Tanf kusa da iyakar Syria da Iraƙi da Jordan.

TRT World