Daraktar Asusun Kula da Ƙananan Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya Catherine Russell ta nuna matuƙar damuwa dangane da yadda rikici ke ƙara ƙaruwa a Lebanon da Isra’ila, musamman bayan wani rahoto da ya nuna cewa wani hari ya kashe aƙalla yara 24 da ke zaune a kudancin Lebanon a ranar Litinin.
"Na damu matuka da yadda ake ci gaba da kai hare-hare a Lebanon da Isra'ila, wanda a safiyar yau aka bayar da rahoton mutuwar akalla yara 24 a kudancin kasar ta Lebanon," in ji ta, tana mai jaddada cewa tashin hankalin na nuni da wani "ƙaruwar hatsari " ga fararen hula a yankin.
Ta yi nuni da cewa, yara a Labanon da Isra'ila na fama da matsananciyar damuwa saboda ci gaba da kai hare-hare ta sama da kuma hijira da suke yi daga gidajensu.
Russell ta bukaci dukkan bangarorin da abin ya shafa da su kiyaye haƙƙin da ya rataya a wuyansu karkashin dokar jin kai ta kasa da kasa don kare fararen hula, ababen more rayuwa, ma'aikatan jin kai, da ma'aikatan lafiya.
Isra'ila ta kaddamar da hare-hare ta sama a kudanci da gabashin Lebanon, inda hukumomin lafiya na kasar Lebanon suka ce akalla mutum 492 ne suka mutu, ciki har da kananan yara 35, yayin da wasu 1,645 suka jikkata a hare-haren da aka kai tun safiyar ranar Litinin, wanda kuma ya tilasta wa dubban fararen hula tserewa daga gidajensu.
Kungiyar Hezbollah da Isra'ila dai na ci gaba da gwabza fada a kan iyakokin ƙasashen tun bayan da Isra’ilar ta ƙaddamar da yaƙi a Zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 41,400, wadanda akasarinsu mata da kananan yara ne.
Sojojin Isra’ila sun ci gaba da matsa ƙaimi inda suke kai hare-hare a Lebanon, tare da yin kunnen uwar shegu da gargaɗin da ƙasashen duniya ke yi kan cewa yaƙin na Gaza zai iya bazuwa zuwa ga sauran yankuna.