Kotun ICC / Hoto: Reuters

Ministan Shari'a na Turkiyya ya yaba wa mai gabatar da ƙara na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Ƙasa da Ƙasa (ICC) Karim Khan bisa neman a kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaronsa, inda ya bayyana matakin a matsayin makararre amma kuma yana da kyau.

A wata sanarwa a shafin X, Yilmaz Tunc ya soki Isra'ila saboda ta'annatin da take yi a Gaza tun 7 ga Oktoban 2023, yana mai ikirarin cewar waɗannan ayyuka sun saaɓ wa dokokin ƙasa da ƙasa tare da keta hakkokin ɗan'adam, ciki har da haƙƙokin rayuwa, mallaka, tsaro da 'yancin yin addini da bayyana aƙida.

Tun ya ce "Bayyana buƙatar neman a kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaronsa Yoav Gallant a gaban Kotun Ƙasa da Ƙasa Mai Hukunta Manyan Laifuka (ICC) bisa aikata laifukan yaki ya zo a makare amma kuma abu ne mai kyau."

Ya yi kira ga kotun ta gurfanar da jami'an gwamnatin Isra'ila da ke da alhakin kai wa mutanen da babu ruwansu hare-hare da zarar kotun ta dawo zama.

Alhakin aikata muggan laifuka na Netanyahu da Gallant

"A matsayinmu na Turkiyya, za mu ci gaba da ganin ana ta tattaunawa kan muggan laifukan cin zarafin ɗan'adam da Isra'ila mai kama-wuri-zauna ke yi, kuma za mu ci gaba da kasancewa tare da 'yan'uwanmu Falasɗinawa," in ji Tunc.

Tun da fari, Khan ya shigar da buƙata a gaban kotun ICC na a kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaronsa Yoav Gallant da shugabannin Hamas uku, ciki har da shugaban siyasar ƙungiyar Ismail Haniyeh.

A wata sanarwa da Khan ya fitar ya ce yana da ƙwararan dalilai da ke nuna cewa Netanyahu da Gallant sun aikata laifukan yaƙi a yankunan Falasɗinawa, musamman a yankin Gaza da aka mamaye tun daga 8 ga Oktoban shekarar bara.

Ya kara da cewa ofishinsa ya miƙa buƙatar neman kama wasu shugabannin Hamas uku - ciki har da Haniye tare da Yahya Sinwar da Mohammed Delf saboda laifukan yaƙi da aka aikata a Israi'la da Gaza tun daga 7 ga Oktoban, 2023.

Isra'ila ta kashe sama da Falasɗinawa 35,000 a Gaza tun 7 ga Oktoba bayan Hamas ta kai mata wani harin kan iyaka da ya zuwa yanzu ta kashe 'yan Isra'ila 1,200. Hare-haren sama da kasa sun mayar da yankunan Falasɗinawa kamar wata bolar zubar da ɓaraguzan gine-gine, wanda hakan ya janyo raba mutane da dama da matsugunansu tare da ƙarancin kayan more rayuwa.

Lamarin ya kuma janyo shari'a a Kotun Ƙasa da Ƙasa da ke Hukunta Manyan Laifuka, wadda a watan Janairu ta bayar da umarni ga Tel Aviv da ta tabbatar da cewa mayaƙanta ba su aikata kisan kiyashi ba kuma sun tabbatar da bayar da damar kai kayan agaji zuwa yankin Gaza.

TRT World