1401 GMT — Tsananin ƙishi ruwa na damun Falasɗinawa a Gaza: Jami'ai
Mummunan ƙarancin ruwa na ƙara ta'azzara yanayin rayuwa ga Falasdinawa a birnin Gaza yayin da aka lalata mafi yawan rijiyoyi da layukan ruwa a ci gaba da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa yankin.
"Mazauna birnin na fama da ƙarancin ruwa da kuma ƙishi ruwa mai tsanani sakamakon lalata rijiyoyi da layukan ruwa," in ji karamar hukumar ta Gaza a cikin wani takaitaccen bayani.
Kakakin karamar hukumar Housni Mohana ya bayyana cewa, an lalata rijiyoyin ruwa guda 42 da kuma wata matattarar tsaftace ruwan da aka kai a harin da Isra'ila ta kai a birnin Gaza.
A watan da ya gabata, ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya ce fiye da rijiyoyin ruwa 700 a yankin sun daina aiki saboda hare-haren Isra'ila da kuma karancin mai. "Wannan yana kara yiwuwar kara zurfafa yunwa da ƙishi ruwa a tsakanin fararen hula," in ji ta.
1347 GMT — Rasha ta yi kira da a gaggauta dakatar da ayyukan sojin Isra'ila a Gaza
Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov ya bayyana cewa, kasar Rasha ta yi kira da a gaggauta dakatar da kai farmakin da sojojin Isra'ila ke kaiwa Gaza.
Da yake magana a wani taron manema labarai a birnin Nizhny Novgorod da ke yammacin Rasha, wanda aka watsa kai tsaye ta shafin intanet na Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar, Lavrov ya ce mataki na gaba bayan tsagaita wuta ya kamata ya zama tattaunawa ce kan kafa kasar Falasdinu.
"Mun yi imanin cewa dole ne a dakatar da aikin (sojojin Isra'ila) nan da nan, a tabbatar da tsagaita wuta, da kuma magance matsalolin jinƙai cikin gaggawa. Sannan ba tare da ɓata lokaci ba, dole ne mu matsa zuwa warware matsalar yankin bisa kafa kasashe biyu - Isra'ila da Falasdinu,” Lavrov ya jaddada.
0813 GMT — Hamas ta amince da ƙudurin Kwamitin Tsaro na MDD kan tsagaita wuta kuma a shirye take ta tattauna kan lamarin, in ji wani babban jami'in ƙungiyar Sami Abu Zuhri a hira da Reuters.
0811 GMT — Sanarwar Hamas ta goyon bayan ƙudurin MDD kan tsagaita wuta 'alama ce mai ƙarfafa gwiwa' — Blinken
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce sanarwar da Hamas ta fitar ta goyon bayan ƙudurin tsagaita wuta a Gaza na MDD 'alama ce mai ƙarfafa gwiwa'.
Blinken ya ce ranar Talata da rana za a ci gaba da tattaunawa game da shirin tsagaita wuta a Gaza da kuma a kwanakin da ke tafe. "Yana da matuƙar muhimmanci a aiwatar da wannan ƙuduri."
0208 GMT — Jordan za ta ƙarɓi baƙuncin wani taro kan buƙatar agajin gaggawa sakamakon hare-haren da Isra'ila ta shafe wata takwas tana kai wa Falasɗinawa a Gaza da aka mamaye, inda Isra'ila take yi wa mutane azaba da yunwa take kuma kashe waɗanda babu ruwansu.
Taron yana fatan tattaro shugabannin duniya da shugabannin hukumomin ba da agaji don "tantance hanyoyin da za a haɓaka yadda ƙasashen duniya suke ɗaukar mataki kan mummunan yanayin da jama'a suke ciki a Zirin Gaza," kamar yadda hukumoin Jordan suka bayyana.
Taron, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya da Jordan da Masar suka yi haɗin gwiwa wajen shirya gudanar da shi a gaɓar Tekun Bahar Mayyit, zai samu halartar Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken da Shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Jordan ta ce taron zai tattauna "shirye-shiryen farfaɗo da Gaza na farko-farko, zai kuma nemi a yi alƙawura kan yin aiki tare bisa tsari don tunkarar mummunan yanayin da jama'a suke ciki a Gaza".
"Babbar manufar wannan taron shi ne cim ma matsaya kan matakan da za a ɗauka don kula da buƙatun da ake da su na yanzu-yanzu" a Gaza, kamar yadda ma'aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa.