Donald Trump ya caccaki Joe Biden inda ya ce shi ne shugaban ƙasa "mafi muni" a tarihin Amurka. / Hoto: AFP

Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya shaida wa wani gangamin yaƙin neman zaɓe a Jihar Ohio kan zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a watan Nuwamab zai kasance “mafi muhimmanci” ga tarihin Amurka.

Kwanaki bayan tabbatar da matsayinsa na dan takarar jam'iyyar Republican, tsohon shugaban ƙasar ya yi gargaɗi kan cewa za a “zubar da jini” idan ba a zaɓe shi ba -- sai dai babu tabbaci kan abin da yake nufi da hakan, inda ya yi wannan batu a lokacin da yake mayar da martani kan batun barazana ga kamfanonin ƙera motoci na Amurka.

“Ranar -- ku tuna da ita, 5 ga Nuwamba -- Ina ga za ta kasance rana mafi muhimmanci ga tarihin ƙasarmu,” kamar yadda Trump mai shekara 77 ya shaida wa waɗanda suka fito gangamin a ranar Asabar a Vandalia da ke Ohio.

A lokacin gangamin, ya caccaki abokin hamayyarsa Joe Biden inda ya ƙara jaddada cewa Biden ɗin ne shugaban ƙasa mafi muni a tarihi.

Da yake sukar abin da ya ce China na shirin ƙera motoci a Mexico da kuma sayar wa Amurkawa, ya ce: “Ba za su iya sayar da wadannan motocin ba idan aka zabe ni. “A yanzu idan ba a zaɓe ni ba zubar da jini zai shafi kowa, hakan zai kasance abu mafi ƙaranci, zai kasance zubar da jini ga duka ƙasa. Hakan zai zama abu mafi ƙaranci. Amma ba za su sayar da waɗannan motocin ba.”

A farkon watan nan, Trump da Biden dukansu sun samu isassun wakilan jam’iyya waɗanda za su ba su damar samun tikitin tsayawa takara a jam’iyyunsu.

Sai dai ana ganin wannan zaɓen na daga cikin zaɓuka mafi tarihi a Amurka sakamakon dukansu waɗanda za su kara kowane daga cikinsu ya ɗanɗana kujerar shugabancin ƙasar.

AFP