Mahalarta taro kan diflomasiyya na Antalya Diplomacy Forum (ADF) sun bayyana baki-biyu da manyan ƙasashen duniya suke yi game da batutuwa daban-daban, tare da yin watsi da dokokin ƙasashen duniya, a cewar Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan.
Da yake jawabi na rufe taron na ADF ranar Lahadi, wanda aka gudanar a kudancin Turkiyya, Hakan Fidan ya ce ana gudanar da muhimmiyar tattaunawa da zummar ganin an tsagaita wuta a Gaza kafin soma azumin watan Ramadan.
Ya ƙara da cewa Turkiyya tana goyon bayan yanayin da zai kawar da tsarin ƙasashen duniya a kan Gaza domin a samar da mafita a yankin.
Fatan tattaunawa don tsagaita wuta a Ukraine
Fidan ya ce Turkiyya tana fata a tattauna domin tsagaita wuta a Ukraine.
"Ya kamata a soma tattaunawa domin tsagaita wuta (a Ukraine). Hakan ba ya nufin a yarda da mamaya, amma ya kamata a tattauna daban game da ƴancin gashin kan ƙasa, da kuma batun tsagaita wuta shi ma daban," in ji Fidan.
Haka kuma Fidan ya ce ana shirin tafiya Amurka a makon gobe bayan da ya samu gayyata daga Sakataren Harkokin Wajen ƙasar Antony Blinken don yi taro na musamman.