Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana ƙwarin gwiwarsa ta kakkaɓe duk wata barazanar ƙungiyoyin ƴan ta'adda ba kawai a ƙasar ba, har ma da duka yankin a nan gaba.
"A shirye muke mu nuna cewa ta'addanci ba shi da mazauni a makomar Turkiyya da ma yankinta. Zaɓen da aka gudanar na baya-bayan na ya ƙara mana ƙaimi," in ji Erdogan yayin da yake jawabi a wani taron buɗa-baki da ya gudanar a shugabannin jami'an tsaro a Ankara ranar Laraba.
Ya jaddada cewa ta'addanci lamari ne da babu ruwansa da ra'ayinka na siyasa don haka ya kama a ɗauke shi da muhimmanci.
Erdogan ya ce dukkan ƙungiyoyin ta'addanci, da suka haɗa da PKK, FETO, Daesh, da DHKP-C, "maƙiyan" al'ummar Turkiyya ne.
A kusan shekaru 40 da PKK - wadda Turkiyya da Amurka da Tarayya Turai suka ayyana a matsayin ƙungiyar ta'addanci - ta kwashe tana yaƙi da Turkiyya ta kashe mutum sama da 40,000, ciki har da mata da ƙananan yara da jarirai.
FETO da shugabanta da ke zaune a Amurka Fetullah Gulen sun kitsa juyin mulkin da bai yi nasara ba na ranar 15 ga watan Yulin 2016 a Turkiyya, inda aka kashe mutum 252 sannan aka jikkata 2,734.