Mutane sun rika gudanar da zanga-zanga ta Allah wadarai da masu kona Alkur'ani mai tsari a Denmark da Sweden kamar wannan gangamin da aka yi a birnin Sanaa, Yemen ranar 24 ga Yuli, 2023. / Hoto: AA Archive

Matakin da mahukuntan Sweden suka dauka na bari ana kona Alkur'ani mai tsarki a watanni tara da suka gabata ya sa kasar ta yi asarar kusan $200,000, a cewar wata kafar watsa labarai ta kasar.

Kona Alkur'ani da wani dan siyasar Sweden dan asalin Denmark Rasmus Paludan ya yi, da kuma wanda Salwan Momika, wani dan gudun hijirar Iraki da ke zaune a Stockholm ya yi, sun sa Sweden ta yi asarar 2.2 m na kudin kasar wato Swedish krona ( $199,300), a cewar gidan rediyon Sveriges.

Wadannan ayyukan masha'a sun sa hukumomi sun tura karin 'yan sanda domin bayar da tsaro da kuma katse tsarin ayyukansu, in ji rahoton da gidan rediyon ya bayar.

Labari mai alaka: Turkiyya ba za ta lamunci kona Alkur’ani ba: Erdogan

- Lokutan da aka kona Alkur'ani a Sweden

Sweden da Denmark sun fuskanci gagarumar suka da Allah wadai daga kasashen duniya sakamakon bayar da izinin kona Alkur'ani ga wasu mutane, har ma da ba su kariyar 'yan sanda.

Paludan, shugaban jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi ta Stram Kurs, ya kona kwafi-kwafi na Alkur'ani a biranen Malmo, Norrkoping, Jonkoping, da Stockholm, ciki har wadanda ya kona a lokacin bikin Easter na shekarar da ta wuce.

Ranar 21 ga watan Yuni, ya kona Alkur'ani a wajen ofishin jakadancin Turkiyya da ke Sweden.

Momika ya ja hankalin duniya mako daya bayan haka, lokacin da ya kona Alkur'ani a wajen wani masallaci a birnin Stockholm lokacin Babbar Sallah.

Ranar 20 ga watan Yuli, ya jefar da Alkur'ani a wajen ofishin jakadancin Iraki da ke Sweden tare da tutar Iraki sannan ya tattaka su.

Kazalika ranar 31 ga watan Yuli ya kona Alkur'ani a wajen ginin Majalisar Dokokin Sweden.

Shi ma wani dan gudun hijirar Iran Bahrami Marjan ya kona Alkur'ani a garin Angbybadet da ke kusa sa birnin Stockholm ranar 3 ga watan Agusta.

Haka kuma Momika ya sake kona Alkur'ani a wajen ofishin jakadancin Iran da ke Sweden a farkon watan Agusta, sannan ya sake kona wani Alkur'anin a wajen Masallacin Stockholm a makon jiya.

Duk da yake wadannan ayyukan rashin mutunci suna zubar da kimar Sweden a idanun duniya da kuma jefa jami'an tsaro cikin hatsari, hukumomin kasar sun bai wa Momika izinin kona kwafi-kwafi na littafin mai tsarki.

Hukumomin tsaron Sweden sun ce yanayin tsaron kasar ya tabarbare tun bayan da gwamnati ta bai wa mutane damar kona Alkur'ani.

AA