Turkiyya ta saka wa Swidin da Finlan sharudda kafin ta amince su zama mambobin kawancen NATO/ Hoto: TRT World

Majalisar Dokokin Sweden ta amince da sabuwar dokar yaki da ta’addanci, wadda ake wa kallon wani muhimmin mataki da zai sanya Turkiyya amince wa Sweden din ta zama mambar kawancen NATO.

Dokar da aka amince a ranar Larabar nan za ta fara aiki daga ranar 1 ga Yuni, kuma za ta bai wa mahukunta damar kamawa tare da daure duk wasu masu goyon bayan kungiyoyin ta’addanci.

Za a iya yanke hukuncin dauri har na shekara hudu ga wadanda suka aikata ta’addanci ko suka hada kai da ‘yan ta’adda. Wannan ya hada da wadanda suka yi wasu abubuwa na nuna goyon baya ga kungiyoyin ta’adda.

Idan akwai dalilai na damuwa, hukuncin aikata hakan zai kai har tsawon shekaru biyu a kurkuku, idan ta kama ma a kara yawan sa zuwa shekaru hudu.

Wadanda suka aikata muggan laifuka kamar samar da makamai, alburusai da kayan fashewa ga ‘yan ta’adda, bayar da mafaka ko hayar wajen zama ga kungiyoyin ta’addanci za su iya fuskantar dauri na shekaru hudu.

Idan akwai dalilai na damuwa sosai game da wadannan manyan laifuka, hukuncin zai kasance daga shekara 1.5 zuwa 7.

Yunkurin Swidin na shiga NATO

Bayan fara rikicin Rasha da Yukren a watan Fabrairun shekarar da ta gabata, Finlan da Swidin sun yanke hukuncin shiga kawancen NATO tare da barin akidar nisantar kawancen sojin da suke da ita ta tsawon shekaru.

Amma kuma Turkiyya da take mambar NATO sama da shekaru 70, ta bukaci kasashen biyu da su dauki kwararan matakan yaki da kungiyoyin ta’adda irin su PKK da FETO matukar suna son zama mambobin kawancen.

A watan Yunin shekarar da ta gabata, Finland da Sweden suka sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Turkiyya don magance damuwar da Ankara ke da ita kan batun tsaro, kuma manyan jami’an diflomasiyya daga kasashen uku sun gana da juna a lokuta daban-daban tare da tattauna yadda za a aiwatar da yarjejeniyar.

A watan Maris, gwamnatin Turkiyya ta bayyana cewa za ta amince da bukatar Finland ta shiga NATO, inda ta kara da cewa Finland ta yi duk abubuwan da suka kamata don zama mamba, amma Sweden na da sauran aiki.

A ranar 31 ga Maris, Majalisar Dokokin Turkiyya ta amince da bukatar Finland ta zama mambar NATO.

Tsawon shekaru sama da 35 da suka gabata, PKK da kasashen Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin kungiyar ta’adda na aikata ta’addanci a Turkiyya inda ta kashe sama da mutum 40,000 da suka hada da mata da yara kanana.

TRT World