Sweden ta bayyana cewa ba ta yi wani shiri na kawo sauyi kan dokar ‘yancin bayyana ra’ayi a kasar ba, kuma ta yi kokarin tsaurara bincike a kan iyakokinta saboda yadda tsaro ya tabarbare, sakamakon kona Alkur’ani Mai Tsarki da aka yi.
“Mun tsaya don kare martabar ‘yancin bayyana ra’ayi na jama’ar Sweden,” in ji Firaminista Ulf Kristersson.
Amma ya bayyana cewa akwai bukatar kowa ya yi amfani da wannan ‘yanci cikin ladabi da sanin ya kamata.
“A kasa mai ‘yanci kamar Sweden, kuna da ‘yanci babba. Wannan ‘yanci mai girma ya dace a aiwatar da shi da sanin ya kamata." in ji Kristersson.
Ya kuma ce gwamnati za ta ‘karfafa’ tsaron kan iyakokin kasar saboda tabarbarewar tsaro.
“Mutanen da ba su da alaka ta kusa da Sweden kar su zo Sweden su aikata muggan laifuka,” Firaminista Ulf Kristersson ya fada wa taron ‘yan jarida, inda ya kara da cewa "nan da Alhamis za a tsaurara matakan tsaro a kan iyakoki.”
A ranar Litinin, wasu mutane biyu haifaffun Iraki – Salwan Momika da Salwan Najem - suka kona Alkur’ani Mai Tsarki a gaban majalisar dokokin Sweden.
A baya mutanen biyu sun taba gudanar da wannan danyen-aiki a wajen babban Masallacin Stockholm da ofishin jakadancin Iraki a babban birnin Sweden, lamarin da ya janyo la’anta daga kowanne bangare.
Wadannan matakai sun sanya dubban mabiya mazhabin Shia a Iraki sun kutsa ofishin jakadancin Sweden a Bagadaza har sau biyu, inda a karo na biyu suka cinna masa wuta.
Ministan Shari’a Gunnar Strommer ya ce ma’anar karfafa bincike kan iyakoki ita ce a tsaurara matakan tsaro don duba sosai ga mutanen da ke shiga Sweden daga sauran kasashen Schengen.
Ya shaida wa manema labarai cewa “Ayyukan tantancewa da bincike a kan iyakoki na ba mu damar tantance matafiya masu shigowa kasar daga sauran kasashen Schengen.”
‘Barazanar tsaro’
Sweden ta sake kaddamar da tsaurara bincike a kan iyakoki a watan Mayun 2022 sakamakon tabarbarewar tsaro.
Strommer ya kuma bayyana cewa sabon tsarin zai fara aiki a ranar Talata inda aka bai wa ‘yan sanda karin damar bincika da tantance mutane a iyakokin Sweden, har da bincikar jiki da ababen hawa.
Strommer ya kuma ce “Manufar ita ce a karfafa ayyukan ‘yan sanda da riga-kafin barazanar tsaro da za a iya kawo wa kasa.”
A ranar Litinin Kungiyar Hadin kan kasashen Musulmi da ke hediwakta a Jeddah ta bayyana ‘bacin ranta’ ga Sweden da Denmark kan yadda suka gaza daukar matakin a zo a gani bayan mummunar aika-aikar kona Alkur’ani Mai Tsarki.