Macron ya shaida wa manema labarai a ranar Juma'a cewa jakadan kasar a yanzu yana dogara ne a kan "abin da sojojin suke ba shi." Hoto: Reuters

Shugaba Emmanuel Macron ya ce sojojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar sun yi garkuwa da jakadan Faransa a ofishin jakadancin kasar, tare da zargin sojojin da toshe hanyar kai kayan abinci ga ofishin.

Macron ya shaida wa manema labarai a ranar Juma'a cewa jakadan kasar a yanzu yana dogara ne a kan "abin da sojojin suke ba shi."

"A yanzu da muke maganar nan, akwai jakadanmu da kuma wani jami'in diflomasiyya da suke tsare a ofishin jakadancin Faransa," in ji shi.

"Sun hana a kai kayan abincin," ya ce, yana mai magana a kan shugabannin sojin Nijar din. "A yanzu abincin da suka ba shi yake ci."

Shugabannin mulkin sojan Nijar sun shaida wa Jakadan Faransa Sylvain Itte cewa ya bar kasar tun bayan da suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum ranar 26 ga watan Yuli.

Amma har wani wa'adi na awa 48 da aka ba shi na ficewar ya wuce, bai bar kasar ba, saboda gwamnatin Faransa ta ki bin umarnin don ta ki amincewa da gwamnati mulkin sojan a matsayin halastacciya.

Faransa da mafi yawan makwabtan Nijar sun yi Allah wadai da juyin mulkin.

Macron ya ce jakadan "ba zai iya fita ba, saboda an nuna ba a son sa kuma ana hana shi abinci."

'Tsokana'

Da aka tambaye shi ko Faransa za ta duba yiwuwar mayar da jakadan gida, sai Macron ya ce: “Zan yi duk wani abu da muka amince da shi ni da Shugaba Bazoum saboda shi ne halastaccen shugaban kasa kuma ina magana da shi a kullum.”

Faransa ta jibge sojoji kusan 1,500 a Nijar, kuma a farkon watan nan ta ce za ta tattauna duk wani batun janye su ne da Bazoum.

Sabbin shugabannin kasar sun yi watsi da duk wasu yarjejeniyoyin hadin kai na soji da Faransa tare da umartar dakarunta su fice ba tare da bata lokaci ba.

An shafe makonni Macron yana yin watsi dsa kira kan kawar da jakadan Faransa, wani mataki da Kungiyar Tarayyar turai ke goyon bayansa da aka bayyana a matsayin bukata ta “neman tsokana.”

Kamar Faransa, in ji mai magana da yawun harkokin wajen EU Nabila Massrali a watan da ya gabata, EU ma ba ta dauki hukumomin da suka kwace mulki a Nijar a "matsayin halastattu ba."

Yankin Sahel da ke kusa da Sahara ya sha fama da abin da Macron ya kira annobar juyin mulki a ‘yan shekarun nan, inda gwamnatocin soji suka hambarar da zababbu na farar hula a kasashen Mali da Burkina Faso da Guinea da kuma Nijar.

TRT Afrika