1438 GMT — Hamas ta kafa sabbin sharuɗɗa a cikin yarjejeniyar 'magunguna ga wadanda take garkuwa da su'
Wani babban jami'in kungiyar Hamas ya sanar da sabbin sharuddan isar da magunguna ga mutanen da kungiyar ta yi garkuwa da su a Gaza, yana mai dagewa cewa manyan motocin da ke dauke da magungunan dole ne Isra'ila ta duba su.
A karkashin yarjejeniyar da masu shiga tsakani Qatar da Faransa suka yi a ranar Talata, za a ba da magunguna tare da taimakon jinƙai ga fararen hula a Gaza domin isar da magungunan da mutanen da ake garkuwa da su ke bukata.
Ana sa ran mutane 45 da aka yi garkuwa da su za su karbi magunguna bisa yarjejeniyar. Musa Abu Marzuk, jigo a ofishin siyasa na kungiyar Hamas, ya bayyana sabbin sharuddan isar da magunguna ga wadanda aka yi garkuwa da su.
"A kowane akwatin magani da ya shiga gare su, to akwatuna 1,000 za su tafi ga mazauna Gaza," in ji shi a shafin X. Marzuk ya ce za a ba da magungunan ne ta wata kasa da Hamas ta amince ba Faransa ba.
1243 GMT — MDD ta yi gargadin mummunar makoma ga Falasdinawa a Gaza bayan yakin Isra'ila
Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Philippe Lazzarini, ya yi gargadi kan mummunar makoma da ke fuskantar Gaza bayan yakin da Isra'ila ke yi a yankin.
Bayan ziyararsa ta hudu a yankin Falasdinu tun bayan barkewar yakin a ranar 7 ga watan Oktoba, babban jami'in na UNRWA ya ce mazauna yankin da dama ba sa tunanin samun wata "makoma a Gaza".
Lazzarini ya shaida wa manema labarai a Birnin Kudus cewa, "Kuna da dubban mutane da ke zaune a kan titi, suna zaune a cikin wadannan tantuna na roba, suna kwana a kan siminti."
The majority of Gaza's 2.4M residents have been forced from their homes, while Lazzarini said more than 60 percent of buildings are estimated to be damaged.
Mafi akasarin mazauna Gaza miliyan 2.4 an tilasta musu barin gidajensu, yayin da Lazzarini ya ce sama da kashi 60 na gine-gine an kiyasta lalacewa.
1246 GMT — Sojojin Isra’ila sun lalata makabarta, sun tono gawawwaki a Khan Younis
Janyewar sojojin Isra’ila daga yankunan birnin Khan Younis ya nuna irin barnar da sojojin suka yi a makabartar inda suka tona kaburbura da dama.
Wakilin kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ce sojojin na Isra’ila sun janye da safiyar Litinin inda suka bar yankin da asibitin Khan Younis Nasser yake.
Ya bayyana cewa sojojin sun lalata makabartar tare da tono kaburbura tare da amfani da buldoza domin lalata wasu wurare a cikin makabartar.
1120 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa uku kusa da sansanin ƴan gudun hijira na Balata
Akalla Falasɗinawa uku harin Isra’ila ta kashe a wani hari ta sama da sojojinta suka kai a cikin wata mota a a kua da sansanin ƴan gudun hijira na Balata da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na WAFA ya tabbatar.
Kungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent ta bayyanacewa ta yi kokari ta kai dauki bayan dakarun na Isra’ila sun janye daga wurin inda suka gano gawarwakin matasan.
Zuwa yanzu Isra’ila ta kashe sama da mutum 24,000 a Gaza.
0825 GMT — 'Yan sandan Isra'ila sun tarwatsa zanga-zangar Yahudawa masu adawa da yakin Gaza
‘Yan sandan Isra’ila sun tarwatsa wata zanga-zanga da aka gudanar a birnin Tel Aviv na Isra’ila inda masu zanga-zangar ke nuna rashin goyon bayansu kan yakin da sojojin kasar ke ci gaba da yi a Gaza.
Jaridar Haaretz daily ta ruwaito cewa ‘yan sanda sun yi amfani da karfi domin murkushe masu zanga-zangar inda suka yi ikirarin cewa zanga-zangar “tana cutar da tunanin jama'a.”
‘Yan sandan sun yi ikirarin cewa taron an yi shi ne ba bisa ka’ida ba inda aka ga ‘yan sandan suna kwace tutocin masu zanga-zangar.
0745 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 13 a Khan Younis
Akalla Falasdinawa 13 Isra’ila ta kashe a hare-haren da ta kai Khan Younis da ke kudancin Gaza, kamar yadda wani rahoto ya bayyana.
Bayan haka akwai kuma wasu gomman Falasdinawan da suka samu rauni a hare-hare ta sama da kasa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasdinu WAFA ya tabbatar.
Haka kuma ya ce jiragen yakin na Isra’ila sun kai hari kan gidajen Falasdinawa a yammacin Khan Younis.